Shugaba Jonathan ya na daure wa rashawa gindi – Tambuwal
Shugaban Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal, ya ce dabi’ar ko in kula da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ke nunawa tana daure wa rashawa gindi a kasar nan. Alhaji Aminu Tambuwal yana magane ne kan “Rawar ’yan majalisa wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya” a wani taron yini daya domin bikin Ranar Yaki da […]
Shugaban Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal, ya ce dabi’ar ko in kula da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ke nunawa tana daure wa rashawa gindi a kasar nan.
Alhaji Aminu Tambuwal yana magane ne kan “Rawar ’yan majalisa wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya” a wani taron yini daya domin bikin Ranar Yaki da Rashawa ta Duniya da kungiyar Lauyoyi ta kasa (NBA) ta shirya a Abuja.
Ya ce, “dauki misali da binciken kudin tallafin mai da na fansho da na Hukumar Hannun Jari ta kasa (SEC) da kuma na kwanan nan matsalar sayen motoci masu sulke. Bayan Majalisar Wakilai ta yi aikin da ya kamata wajen bincikar matsalolin, sai ka ga wani abu daban lokacin da aka zo batun hukuntawa. A wasu lokuta, sai ka ga gwamnati tana kafa wasu kwamitoci don maimaita aikin da majalisa ta riga ta yi. dauki misali da sayen motoci masu sulke, Mashawarcin Shugaban kasa kan harkokin tsaro, kalubalen tsaron da suke addabar kasar nan, bai kamata a dora masa wani aiki da zai fi kyau a mika wa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ba.”
Ya kara da cewa, “Ba aikin gwamnati ba ne ta kafa kwamiti a lamarin da a fili yake ga daukacin ’yan Najeriya. Abin da ya kamata Shugaban kasa ya yi shi ne kawai ya umarci EFCC ta binciki lamarin. Idan Shugaban kasa ya ba da umarni ina da yakinin muna da mutanen kirki a EFCC da za su yi aiki mai kyau. Amma kafa kwamitoci na daban a matsalolin da suke a fili, dabi’ar Shugaban kasar na ko in kula bai taimakawa wajen yaki da cin hanci.”
Shugaban majalisar ya ce hukumomin gwamnati da daidaikun jama’a suna yawan karya dokokin yaki da rashawa. Ya ce, “Jerin yadda rashawa ke aukuwa musamman a huku-momin gwamnatin Najeriya, sun hada da karkatar da dukiyar gwamnati zuwa aljifan jama’a, zumurken kudin kwangila, cin hanci ciwo bashi na karya da yin alfarma da biyan bashi na karya da kwace kadarorin gwamnati da magudin zabe da kare maciya rashawa da sauransu.” Ya ce majalisar dokoki ce ta bude kofar yaki da rashawa ta hanyar kafa dokar amincewa da kafuwar hukumomin EFCC da ICPC tare da ba su cikakken iko na bincike da hukuntawa.
Ya ce, binciken jin ra’ayin jama’a a kafafen sadarwa na intanet ya nuna kashi 98 cikin 100 na ’yan Najeriya da suka tofa albarkacin bakinsa game da matakin da Najeriya take kai kan rashawa ya nuna suna jin Hukumar Tabbatar da Amana ta Duniya (TI) ta yi wa Najeriya sauki.
Sai dai kakakin Shugaban kasa Dokta Rueben Abati ya bayyana kalaman na Tambuwal a matsayin “abin takaici.”
Dokta Abati wanda ya mayar da martani ta tiwitarsa mai suna @abati1990 a ranar Talata da safe ya ce, “Ina jin abin takaici ne a ce mutumin da ke rike da wannan babban matsayi ya rika magana kan kawar da kai ko daure gindi…”