Shugaba Jonathan ya yi alkawarin maida hanyar Keffi zuwa Lafiya tagwaye
Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin mayar da hanyar Keffi zuwa Lafiya zuwa Benuwai tagwaye. Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ne ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata a wajen bikin bude Babbar Kotun Tarayya da ke Lafiya fadar Jihar Nasarawa. Shugaban wanda Mataimakinsa Muhammad Namadi Sambo ya wakilta ya ce bude kotun ya […]
Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin mayar da hanyar Keffi zuwa Lafiya zuwa Benuwai tagwaye. Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ne ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata a wajen bikin bude Babbar Kotun Tarayya da ke Lafiya fadar Jihar Nasarawa.
Shugaban wanda Mataimakinsa Muhammad Namadi Sambo ya wakilta ya ce bude kotun ya nuna kudirinsa gwamnatinsa na inganta bangaren shari’a inda ya ce Babban Kotun Tarayyar tana daga cikin manyan kotuna uku da gwamnatinsa ta kaddamar cikin shekara biyu da suka gabata.
Shugaban ya bukaci bangaren shari’a ya sauke nauyi da ya rataya a wuyansa ba tare da saba wa ingancin aiki ba.
Shugaban ya ce an amince da bukatun da gwamnatin jihar ta mika na neman a samar mata da karamar tashar samar da wutar lantarki mai karfin KbA 330.
Tun farko a jawabinsa Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya nemi tallafin Gwamnatin Tarayya don magance matsalolin rashin tsaro da jihar ke fuskanta a yanzu.
A jawabi Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Lafiya Malam Ibrahim Indayi Auta ya ce kafa kotun wata shaida ce na aikata adalci a kasar nan kasancewar Babbar Kotun ta Tarayya tana da rassa 30 da alkalai sama da 50.
Abubuwa da aka gudanar a wurin bikin sun hada da kaddamar da duba sassan daban-daban na babban kotun da Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo ya yi.
Ziyarar Shugaban kasar ta ba gwamnatin jihar damar bayyana dimbin nasarori da ta samu a shekara biyu da suka gabata, inda aka kaddamar da makarantar zamani ta Ta’al da wasu sababbin hanyoyi da gwamnatin Al-Makura ta yi a Lafiya.
Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo wanda ya kaddamar da ayyukan a madadin Shugaba Jonathan ya kwatanta bikin a matsayin mai dimbin tarihi inda ya yaba wa Gwamna Umaru Al-Makura a wadannan bangarori.