Shugaba Jonathan ya yi wa majalisarsa garambawul
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yi garambawul ga Majalisar Zartarwarsa a shekaranjiya Larabar bayan da wasu ministoci suka ajiye mukamansu a makon jiya. Ministoci bakwai ne suka ajiye aikin su a makon jiya, wadanda suka hada da Ministan Lafiya, Onyebuchi Chukwu da Minista a Ma’aikatar Neja-Delta, Darius Ishaku da Minista a Ma’aikatar Al’amuran Kasuwanci, […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yi garambawul ga Majalisar Zartarwarsa a shekaranjiya Larabar bayan da wasu ministoci suka ajiye mukamansu a makon jiya.
Ministoci bakwai ne suka ajiye aikin su a makon jiya, wadanda suka hada da Ministan Lafiya, Onyebuchi Chukwu da Minista a Ma’aikatar Neja-Delta, Darius Ishaku da Minista a Ma’aikatar Al’amuran Kasuwanci, Samuel Ortom da Minista a Ma’aikatar Ilimi, Nyesom Wike da Ministan Watsa Labarai, Labaran Maku da Ministan kwadago, Emeka Wogu da kuma Minista a Ma’aikatar Tsaro, Musiliu Obanikoro.
A garanbawul din, Minista a Ma’aikatar Harkokin kasashen Waje, Nurudeen Mohammad zai kasance Ministan Riko a Ma’aikatar Watsa Labarai, a yayin da Minista a Ma’aikatar Harkokin kasashen Waje, biola Onwuliri ya zama Minista a Ma’aikatar Ilimi.
Shi kuwa Ministan Al’amuran Kasuwanci da Zuba Jari, Olusegun Aganga, yanzu shi zai yi rike ma’aikatar. Haka Ministan Ayyuka na Musamman, zai yi rike Ma’aikatar kwadago da Ingantuwar Aiki. A yayin da Ministan Ma’aikatar Neja-Delta zai kasance Ministan ma’aikatar.