Shugaba kasa da ’yan Majalisa: Ina ’yan matan Chibok?
Yan Majalisar kasaa don Allah wai har sai yaushe ne za ku dauki mataki na kiran Shugaban kasa Goodluck Jonathan, gaban majalisa domin ya yi wa kasa bayani a kan Kisan kare dangi da Ake cigaba da yi wa talakawan Arewa Maso gabas, domin fa ba yau ne ko jiya ake kashe-kashe a Arewa ba […]
Yan Majalisar kasaa don Allah wai har sai yaushe ne za ku dauki mataki na kiran Shugaban kasa Goodluck Jonathan, gaban majalisa domin ya yi wa kasa bayani a kan Kisan kare dangi da Ake cigaba da yi wa talakawan Arewa Maso gabas, domin fa ba yau ne ko jiya ake kashe-kashe a Arewa ba a kashe 20 ko 30 ko 40 ko 50 ko 100 ko 200, har mutum sama da 300, an kashe a Arewa, amma ko sau daya ba mu taba ganin kun kira shugaban kasa ya zo majalisa ya yi wa ’yan kasa bayan in mene ne gwamnatinsa ke yi, domin kawo karshen wannan kashe mutane a duk rana.
A yi wa kasa bayani kan satar kannen mu mata ’yan makaranta sama da guda 200, a garin Chibok yau sama da kwanaki 64, ke nan babu wata magana da hankali zai dauka akan me gwamnati take yi domin neman ’yan matan nan da aka sace a Barno. Mu dai yanzu sam sam ba mu gamsu da irin matakan da gwamnati take cewa tana dauka ba.
A gaskiya ’yan majalisar Najeriya wallahi da yawa daga cikinsu sun nuna mana cewa sam-sam ba su ma san mene ne ya kai su ba. Domin dokar kasa ce ta ba su damar kiran shugaban a irin wannan.
Hali, don ya yi musu bayani irin matakan da yake dauka amma Rashin Sanin Makaman Aiki Ya hanasu,
Abun bakin cikin ma shi ne Kan yadda ’yan majalisa suka yarda, kuma suka amince a kara dokar tabaci a jihohin Adamawa Borno da Yobe har karu na Uku kanda babu Wannan magana na kara Dokan tabaci karu na Uku a dokar kasa,
Kirana ga Gwamnonin Adamawa Borno da Yobe Shine Cewa yanzu Agaskiya yanzu fa Tura takai banga kuma Hakurin Matasa Ya Kare dun haka Lokaci Yayi da Daku Saya wa Matasa Makamai Domun su Kare Kan su da Kasan mu Tunda Soja da ’yansanda sun kasa, kuma sun gaza, na tabbata in har matasa na da makamai za su iya kare kan su da al’ummar su, don bai kamata mu sa ido ana musu irin wannan kisan dauki daidai din ba
Tunda Gwamnatin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ta kasa, kuma ta gaza kare rayuwa da duniyar Jama’a, musamman a Arewa maso Gabas
Mu ‘yan Arewa addu’ar mu ita ce, Allah Ka ceto mana kannen mu daga hannun wadannan mutane
Haka kuma dukkan mai hannu a kan kashe jama’ar Arewa, Ya Allah Ka tona masa asiri Allah Ka wulakanta shi tun a nan duniya. Amin.
Amadu Manager Daga Bauchi Unguwan Karofin Madaki a Nigeria.08065189242.