Shugaba Mahama ya kaddamar da littafi a kan shugabancinsa
A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya gabatar da wani sabon littafi a kan yadda ya gudanar da shugabancin kasar.Littafin wanda ya kaddamar a birnin Accra, ya fayyace irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu ta fuskar tattalin arzikin, inda ya ce kasar tana da kyakyawar makoma.Lokacin da yake […]
A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya gabatar da wani sabon littafi a kan yadda ya gudanar da shugabancin kasar.
Littafin wanda ya kaddamar a birnin Accra, ya fayyace irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu ta fuskar tattalin arzikin, inda ya ce kasar tana da kyakyawar makoma.
Lokacin da yake kaddamar da littafin mai suna, Accounting to the people, shugaban ya ce “Babu shakka ci gaba na samuwa a wurare daban-daban.”
Ya kara da cewa bukatar da ake ita na wutar lantarki na karuwa kuma ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin wutar lantarki ta isa duk kauyuka da biranen kasar.