Shugaba majalisa ya raba wa ’yan kasuwa mata buhunan Shinkafa dubu
Shugaban Majalisar Jihar Edo Honarabul Philip Shaibu ya ba da kyautar buhunan shinkafa dubu ga matan ‘yan kasuwa na Etsako ta tsakiya jihar Edo. Ya yi kyautar ne a matsayin kyautar bikin kirsimeta da aka gudanar a makon jiya, a karshen shekarar da ta gabata, kuma wurare da ya sa aka raba wannan kyautar ta […]
Shugaban Majalisar Jihar Edo Honarabul Philip Shaibu ya ba da kyautar buhunan shinkafa dubu ga matan ‘yan kasuwa na Etsako ta tsakiya jihar Edo. Ya yi kyautar ne a matsayin kyautar bikin kirsimeta da aka gudanar a makon jiya, a karshen shekarar da ta gabata, kuma wurare da ya sa aka raba wannan kyautar ta shinkafar su ne, Jattu da Uazirue da Iyambo da Fugar da Okpella da sauran kauyukan yanki.
Wadanda suka halarci wurin raba wannan kyautar da shugaban Majalisar ya yi, sun ce kowa sai sambarka yake yi masa, har da ainihin maigirma Gwanan Jihar Comrade Adam Oshiomhole, shi ma ya shiga aka dama da shi wajen mika kayan, domin nuna farin ciki ga kyautar ta dan majalisar
Honarabul Shaibu ya ce, wannan kyautar na yi ta bisa dalilin nuna farin ciki ga mata ’yan kasuwa wadanda suka bai wa jam’iyyar APC goyon baya a wannan yankin da jiharmu baki daya. Don haka wannan somin tabi ne ga matan, tunda ina da niyyar yin abin da ya fi wannan, domin kara faranta wa kowa zuciya a jihar tamu saboda mu kara samun goyon baya ga mata da yawa su zabi APC da zuciya daya a zaben 2015. Kuma bai tsaya a nan kadai ba, Honarabul Shaibu ya shirya wa yara su dubu gagarumar liyafa a lokacin wannan kirsimeti a garin Jattu.
A Jihar Dalta, kuma makwabciyar Jihar Edo a can ma wani dan majalisa ne na karamar Hukumar Burutu, Honarabul Joseph Alubeze Fuludu shi kam yaba wa Sanata Ifeanyi Okowa da Honarabul Julius Pondi game da irin abin da ya ce kokarinsu da suka yi a bangaren gwamnati, da kuma na majalisar wakilai a zaben fidda gwani da ya gudana a jihar.
Honarabul Fuludu ya furta hakan ne a makon da ya gabata a garin Asaba hedikwatar jihar, inda ya ce wannan kokari da nasara da ya samu sun tabbatar masa da cewa zai sameta a zaben shekarar 2015, inda ya bayya zaben fidda gwani da aka yi a jihar, cewa, an yi shi cikin tsari; kuma zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana kamar yadda ake bukata inji shi’’.