Shugaba Muhammadu Buhari: Najeriya yake kishi ko Arewa?
Tabbas mu mutanen Arewa, wajibi ne mu so Arewa da zuciya daya, domin ita tamkar uwa ce a wurinmu. Kakarmu kuma ita ce Najeriya, wadda ta haifi Kudanci da Arewaci, ita ma wajibinmu ne mu ba ta girma, domin ita ce ta hada iyayen nan namu guda biyu. Kuma ba za a taba mancewa da […]
Tabbas mu mutanen Arewa, wajibi ne mu so Arewa da zuciya daya, domin ita tamkar uwa ce a wurinmu. Kakarmu kuma ita ce Najeriya, wadda ta haifi Kudanci da Arewaci, ita ma wajibinmu ne mu ba ta girma, domin ita ce ta hada iyayen nan namu guda biyu. Kuma ba za a taba mancewa da tushe ba, idan ana son a samu abin da ake so.
Wannan kasa Najeriya, mai dauke da kabilu mabiya addinai daban-daban da kuma manyan yankuna guda biyu (Kudu da Arewa), akwai alamar raunin tunani ga duk wanda yake ganin cewa, shi ne mafi hakki ko kuma shi kadai yake da hakki a kan arzikin kasa. Ko kuma yake jin cewar dan yankinsa ne kawai ya dace da shugabanci.
Iya abin da ni na sani, tun daga kan su Sardauna har zuwa yau, babu wani dan siyasa guda tak, da za ka ga yana cika yana batsewa, yana kai yana komowa da sunan kare hakkin yankinsa, face ka same shi mutum mafi sharrin da zai fi kowa kawo wa yankinsa ci baya. Wannan ba dan siyasa ba ma kawai, har da mu talakawa masu jefa kuri’a da zauna gari banza ’yan a bi Yarima a sha kida.
Marigayi Sa Abubakar Tafawa balewa, na saurari kalamansa na kamfe da yake yi wa al’umma a kan su zabi jam’iyyarsu ta NPC, wadda wannan jam’iyyar kowa ya san jam’iyya ce ta ’yan Arewa da aka kafa ta domin ci gaban Arewa. Amma a cikin ababen da yake jan hankalin al’umma da shi na su zabi jam’iyyar, shi ne; za su yi duk yadda za su yi su hada hannu da Gwamnatin Tarayya, a gina wata makaranta da za ta hada mutanen Kudu da Arewa, domin su kara samun fahimtar juna.
Ga abin da yake cewa a cikin kalamansa “…Mu NPC, mun dauka maganar ilmi magana ce ta kasa duka, baki daya. Saboda haka za mu yi iyakar kokarinmu, mu hada kai da gwamnatin jihohi, yadda za a dauki karantarwa a makarantu ya zama abu bai daya, a Najeriya duka. Waton bukatarmu ita ce, mu NPC muna son duk ilmin da za a bayar, ya zamana ya amfani kasa ne baki daya. Manufarmu ita ce, a sami mutanen kowace jiha, cikin kowane wurin aiki na Gwamnatin Tarayya. Za mu himmantu, da ba da taimakon kudi, yadda za a yi gine-ginen makarantu. Idan Allah Ya yarda, za mu kafa makarantun sakandare, da na sana’o’i cikin jihohi duka, tare da yardar gwamnatin jiha. Wadanda su makarantun nan, a cikinsu za a sami almajirai daga jihohi duka. Waton mu NPC, mun tabbata haduwar ’yan makaranta wuri guda, yana jawo hada kai kuma zai kara kawo zumunta da soyayya tsakanin kabilun kasar nan na Najeriya…”
Shi Arewar yake yi wa aiki kuma domin ita yake wannan siyasar. Amma a cikin kalamansa, ya mayar da hankali sosai wajen hanyoyin da za su bi domin ganin an wanzar da zaman lafiya tsakanin wadannan kabilun mabiya addinai daban-daban. Kuma an ga turbar alheri da suka dora wannan kasa a kai. Sai dai kuma da yake akwai wasu jam’iyyun siyasa da suka ki yabawa, kuma suka ki kallon wannan jan aikin da suke yi domin hada kan Najeriya, suka ki bari a janye zancen kabilanci da bangaranci. Tun a wancan lokacin ne abubuwa suka fara lalacewa, wannan kasa kawo yanzu.
A shekarar 1963, an gudanar da kidayar jama’a wanda ya nuna yankin Arewa ne ya fi kowane yanki yawan jama’a a kasar. Sakamakon ya jawo rikici tsakanin yankunan Najeriya, inda jam’iyyar NCNC ke ganin an yi hakan ne domin kawai a ba yankin Arewa kujeru mafi yawa a Majalisar Dokoki. Wannan kuma daman ita ce babbar musibar da ke iya tarwatsa al’umma komai girmanta da karfinta. Shi ya sa ma jam’iyyar na fara fitowa da wannan zance, riginginmu suka biyo baya, komai ya dagule.
Bayan da rigingimun suka ki ci suka ki cinyewa, sai sojoji suka yi juyin mulkin farko a ranar 15 ga watan Janairun 1966 (Juyin mulkin da ya kara tarwatsa kasar). Wanda tun daga nan Najeriya ta fara gangarawa suman mutuwarta har zuwa yanzu da ta kawo gargara, wanda idan abubuwa sun ci gaba da tafiya hakan, to sunan Najeriya marigayiya kafin ma zaben 2015, wanda ya canza alkiblar kasar da makomarta.
A ranar Juma’a, 15 ga watan Janairu, 1966: A kokarinsu na kawo karshen rigingimun siyasar da ake ta yi tsakanin jama’a a yankunan Najeriya, wasu sojoji yawancinsu ’yan kabilar Ibo a karkashin jagorancin Chukwuma Kaduna Nzeogwu, suka yi juyin mulki, inda aka kashe Sa Ahmadu Bello da Sa Abubakar Tafawa balewa da Sameul Ladoke Akintola da Ministan Kudi Festus Okotie-Eboh. A wannan lokacin, Dokta Nnamdi Azikiwe na jinya a kasar waje kuma ko shakka babu, ba kishin kasa ne ya haddasar da wannan juyin mulkin ba, kabilanci ne kawai.
Duk da kisan shugabannin da sojojin suka yi a lokacin, gwamnatin Aguiyi-Ironsi ta yi alkawarin kawo karshen rikice-rikicen da ake a kasar da kawo ci gaban kasa da kawar da cin hanci da ma mayar da mulki ga hannun farar hula, lamarin da ya sa jama’a ba shi goyan baya. Amma fa da yake harkar ta riga ta zama kabilanci, kafin ka ce kwabo sai wasu sojojin, musamman wadanda suka fito daga Arewacin Najeriya suka yi wa Aguiyi Ironsi juyin mulki, suka nada Janar Yakubu Gowon a matsayin sabon shugaban mulkin sojin kasar.
Gowon ya yi kokarin kawo zaman lafiya tsakanin gwamnatinsa da ’yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya, tare da cin alwashin mayar da kasar ga hannun farar hula.
A ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 1967, Janar Gowon ya kasa yankuna hudu na Najeriya zuwa jihohi 12, wadanda aka nada gwamnoni su shugabance su. Sai dai shugaban yankin gabashin Najeriya Chukwuemeka Ojukwu bai amince da raba yankunan ba, inda ya ce yankin zai balle ya zama jamhuriya mai cin gashin kai da ya kira Biafra. Yarda da hakan da ba a yi ba, ya jawo yakin basasa tsakanin yankin Biyafara da sauran yankunan Najeriya. An kwashe shekaru uku ana yakin da ya yi sanadiyyar mutuwar jama’a da dama a Najeriya, musamman a yankin Biyafara.
Kai, a haka fa idan ka koro tarihi zuwa yau, za ka samu duk sanadiyyar zubar jini shi ne, wani yanki ne za su fito su ce ba mai ikon yi sai su, ko kuma mabiya wani addini ne da za su fito su ce ba addinin kowa sai nasu. Ta haka ne ake bi ana sace kudinmu ana rabewa, ana turo mana sojoji suna kashewa. Ana kuma kama mu ana kullewa. Kuma ku aza koma waye a kan ma’auni ku gani, idan dai wanda yake fafutukar sai ya kare hakkin yankinsa ne kawai, za ku same shi bai tsinana wa yankin nasa komai ba sai sharri. Kuma ban cire kowa ba (Kudanci da Arewaci).
Najeriya fa kasa daya ce, mai yankuna da kabilu da addinai. Hausawa suka ce, cin kasuwa da makiyi tilas ne. Abin da ba mu sani ba shi ne, ko Janar Buhari da kuke ganin muna so muna kauna, domin yana mai kishin Najeriya ne baki dayanta ba Arewa kadai ba. Kuma wannan ce ta sa muke kallonsa adili, kuma Allah Ya sa muna soyayyarsa a zuciya. Inda dan kishin Arewa ne ita kadai, da kun same shi layi dai da su wane.