Shugaba Obasanjo ya jaddada sakacin gwamnati kan ceto ’yan matan Chibok

Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya jaddada sakacin gwamnati kan ceto’yan matan Chibok, inda ya yi nuni da cewa, “Da Gwamnatin Tarayya ta dauki mataki a cikin lokaci da zuwa yanzu an gano ’yan matan Chibok da aka sace”.Obasanjo ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci wakilan Gidauniyar Obasanjo domin karbar kula da […]

Shugaba Obasanjo ya jaddada sakacin gwamnati kan ceto ’yan matan Chibok
Shugaba Obasanjo ya jaddada sakacin gwamnati kan ceto ’yan matan Chibok

Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya jaddada sakacin gwamnati kan ceto’yan matan Chibok, inda ya yi nuni da cewa, “Da Gwamnatin Tarayya ta dauki mataki a cikin lokaci da zuwa yanzu an gano ’yan matan Chibok da aka sace”.
Obasanjo ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci wakilan Gidauniyar Obasanjo domin karbar kula da Makarantar Firamaren Gwaji ta ’Yan mata da ke Kude a Dutse Jihar Jigawa na tsawon sheakara 10.
Ya ce, “Na so a ce sanya hannu kan wannan yarjejeniya ya zo ne a wani lokaci na daban. A yayin da muke magana a yanzu kan muhimmanci ilimin ’ya’ya mata, muna da ’yan matan da aka sace a Chibok. Ina tausaya wa iyayen yaran ’yan matan.”
Obasanjo, wanda ya yi addu’ar Allah, cikin rahamarSa da tausayawarSa Ya dawo da ’yan matan ga iyayensu cikin koshin lafiya, ya ce kada sace ’yan matan ya karya gwiwar iyaye daga tura su makaranta. Ya ce, Gidauniyar tana aiki a fannin kiwon lafiya baya ga ilimi, kuma tana samar da abinci mai gina jiki da horar da matasa kan shugabanci a Afirka.
Tsohon Shugaban kasar ya ce, karbar makaranta yana nuni ne da muhimmancin ilimin ’ya mace tare da karfafa wa iyaye su ilimantar da ’ya’yansu mata.    
Da yake magana Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce gwamnatin jihar ta kulla yarjejeniyar shekara goma da Gidauniyar Obasanjo da nufin habaka ilimi a jihar.