Shugaba Putin ya sha gaban Obama a karfin ikon duniya – Mujallar Forbes

  Shugaban Rasha bladmir Putin ya sha gaban Shugaban Amurka a karfin mulkin duniya, a cewar mujallar Forbes. Wannan shi ne karo na farko cikin shekara uku da kimar karfin ikon Obama ta yiwo kasa warwas, kamar yadda mujallar ta bayyana a karo na biyu, a daidai lokacin da dangantakar Amurka da Rasha ta yi […]

Shugaba Putin ya sha gaban Obama a karfin ikon duniya – Mujallar Forbes

 

Shugaban Rasha bladmir Putin ya sha gaban Shugaban Amurka a karfin mulkin duniya, a cewar mujallar Forbes. Wannan shi ne karo na farko cikin shekara uku da kimar karfin ikon Obama ta yiwo kasa warwas, kamar yadda mujallar ta bayyana a karo na biyu, a daidai lokacin da dangantakar Amurka da Rasha ta yi tsami.
Mista Putin, ya shafe shekara 12 yana da tasirin karfin mulki a kasar Rasha, kuma an sake zabensa a  matsayin shugaba a watan Afrilun bana.
Shi kuwa Obama ya yi kasa ne a daidai lokacin da aka shafe kwanaki 16, Amurka ta tsaya cik, ba a aiwatar da ayyukan gwamnati, saboda takaddamar kasafin kudi, inda ya yi yunkurin fara aiwatar da shirin kula da lafiya na Obamacare.
Mujallar Forbes, ta yi la’akari da yadda Rasha ta sha gaban Amurka wajen hana a kai wa shugaba Bashar al-Assad na Siriya hari, ta kuma yi uwa da makarbiya a rikicin na Siriya. Don haka mujallar ta bayyana shugaba Putin a matsayin mafi karfin iko a fadin duniya.