Shugaba Rouhani ya yi kiran yin ‘sulhu’ a Gabas ta Tsakiya
Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani ya ce akwai bukatar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya su magance matsalolinsu ba tare da dogara da manyan kasashen waje ba. A ranar Lahadi ne Shugaba Rouhani ya yi kira kamar yadda kafar labarai ta AFP ta ruwaito daga Tehran. “Mun yi imani cewa idan akwai wata matsala a yankin, […]

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani ya ce akwai bukatar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya su magance matsalolinsu ba tare da dogara da manyan kasashen waje ba.
A ranar Lahadi ne Shugaba Rouhani ya yi kira kamar yadda kafar labarai ta AFP ta ruwaito daga Tehran. “Mun yi imani cewa idan akwai wata matsala a yankin, za a iya magance ta ta hanyar sulhu,” inji Rouhani ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi wajen bude wata tashar jiragen ruwa a birnin Chabahar na Kudu maso Gabashin kasar da gidan talabijin din kasar ya watsa.
Ya kara da cewa, “Ba mu bukatar makamai balle sanya hannun manyan kasashen waje. Za mu iya magance matsalolinmu ta hanyar hadin kai da sulhuntawa.”
Kalaman na Rouhani suna zuwa ne bayan ruruwar adawa a tsakanin kasar Iran da ’yan Shi’a ke mulkinta da kuma Saudiyya da sarakunan Sunni suke mulkarta.
Manyan kasashen biyu suna tallafa wa masu adawa da juna a daukacin yankin – musamman a Siriya da Yemen – kuma shugabannin Saudiyya a baya-bayan nan sun yi yunkurin dakile tasirin da Iran ke dada samu a yankin lamarin da ya dada fadada rikicin.
Sai dai Rouhani ya ce nasarar baya-bayan nan da aka samu a kan kungiyar IS, ta ba da kofa ga Gabas ta Tsakiya ta gusa gaba don dawo da martabarta wajen “magance yaki da rikicin da ke aukuwa a tsakanin ’yan Shi’a da Sunni… da kuma kawar da tsoma bakin manyan kasahen waje da ake fama da ita.”
Saudiyya da masu sukar Iran a Yammacin Turai suna zargin Tehramn da kokarin mamaye yankin tare da danne makwabtanta.
Rouhani ya ce: “Babu wata kasa da za ta yi da’awar ta karfi a yankin. Kamar yadda masu manyan kasashe masu karfin makamai ba za su cimma haka ba.”