Shugaba Sisi ya lashi takofin ganin bayan kungiyar ’Yan Uwa Musulmi

Shugaban Masar kuma dan takarar neman shugabacin kasa, Mashal Abdul Fattah el-Sisi ya ce kungiyar ’Yan Uwa Musulmi ba za ta yi saura ba, idan ya lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a karshen watan nan.Sisi ya bayyaana haka ne a wata zantawa da ya yi ta farkon don fara yakin neman zabensa, […]

Shugaba Sisi ya lashi takofin ganin bayan kungiyar ’Yan Uwa Musulmi
Shugaba Sisi ya lashi takofin ganin bayan kungiyar ’Yan Uwa Musulmi

Shugaban Masar kuma dan takarar neman shugabacin kasa, Mashal Abdul Fattah el-Sisi ya ce kungiyar ’Yan Uwa Musulmi ba za ta yi saura ba, idan ya lashe zaben shugaban kasa da za a gudanar a karshen watan nan.
Sisi ya bayyaana haka ne a wata zantawa da ya yi ta farkon don fara yakin neman zabensa, wanda aka yada a wani gidan talabijin din kasar ranar Litinin da ta gabata inda ya ce dawo da zaman lafiya da ci gaba sune abubuwan da zai ba fifiko idan aka zabe shi, wanda hakan zai yuwu ne kawai bayan an kawar da kungiyar daga dorar kasa. Ana ganin matakin nasa na nuni da yadda shugaban ya kudiri aniyar musguna wa kungiyar wanda ita ce kungiyar siyasa mafi girma a kasar.
Tun bayan hanbarar gwamnatin Shugaba Morsi, Shugaba Sisi ya fara murkushe ’yan kungiyar inda wasu ’yan kasar ke masu kallon wani gwarzo, masana kuma na ganin shi ne wanda zai lashe zaben da za a gudanar ranakun 26 da 27 watan nan.
Hamdeen Sabahi shi ne dan takara daya tilo da zai kalubalance shi a zaben. Mista Sabahi dan jam’iyyar gurguzu ne wanda kuma yazo na uku a zaben da ya kai Shugaba Morsi karagar mulki a shekarar 2012.
Yakin neman zaben Shugaba Sisi dai ana ganin za a yi shi ne a boye saboda dalilan tsaro wanda kuma bai rasa nasaba da yadda wasu ke yi masa barazanar kisa. Ya bayyana da kansa cewa sau biyu yana tsallake rijiya da baya. Sai dai kuma bai bayyana ko su waye yake zargi da aikata hakan ba.