Shugaba Trump ya ayyana Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila

Shugaban Amuka Donald Trump ya cika alkawarin da ya yi wa masu goyon bayan Isra’ila na ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar. Trump dai ya yi watsi da kiraye-kirayen da shugabannin duniya suka masa, ciki har da Sarki Salman na Saudiya, wanda ya ce masa matakin zai iya harzuka musulmin duniya. Hakanan ita […]

Shugaba Trump ya ayyana Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila

Shugaban Amuka Donald Trump ya cika alkawarin da ya yi wa masu goyon bayan Isra’ila na ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar.

Trump dai ya yi watsi da kiraye-kirayen da shugabannin duniya suka masa, ciki har da Sarki Salman na Saudiya, wanda ya ce masa matakin zai iya harzuka musulmin duniya.

Hakanan ita Majalisar Dinkin Duniya ta gargadin Trump da cewa irin wannan matakin zai iya kawo cikas a kokarin da ake yi na yin sulhu a yankin Larabawa.

Amma Trump ya yi kunnen Mazuru, inda ya ce “A yau din nan, mun yi abin da ya dace na ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila,” inji Trump.

Jim kadan bayan ayyanawar da Trump, Firayi ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya mika sakon godiya ga Shugaba Trump inda ya ce “Muna godiya ga Shugaba Trump bisa jaijircewarsa.”