Shugaban Ƙasar Laberiya ya rage albashinsa

Shugaba Boakai ya ce matakin ya nuna ƙudurinsa na ƙarfafa riƙon amana.

Shugaban Ƙasar Laberiya ya rage albashinsa

Shugaban Ƙasar Laberiya, Joseph Boakai da kansa ya rage albashinsa da kashi 40 cikin 100.

“Domin cika alƙawarinsa na tabbatar da daidaiton kasafin kuɗi da tsaron kuɗi na ƙasar, Shugaba Joseph Nyuma Boakai, Sr. ya ba da sanarwar rage albashinsa da kashi 40 cikin 100,” in ji wata sanarwa da aka fitar a shafin gwamnatin Laberiya.

Shugaba Boakai ya ce matakin ya nuna ƙudurinsa na ƙarfafa riƙon amana.

“Bugu da ƙari kan batun rage albashin da ya yi, shugaban ƙasar ya yi alƙawarin bai wa Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata (CSA) damar tabbatar da cewa albashin ma’aikata ya yi dai-dai da halin da al’umma ke ciki.

“Sannan kuma ma’aikata za su samu albashi mai kyau saboda gudumawar da suka bayar ga Ƙasar.

“Shugaban Kasa ya yi alkawarin ɗaukar nauyin al’amuran kuɗi da kuma biyan albashi na gaskiya ga ma’aikatan gwamnati a matsayin wani kyakkyawan mataki na bunƙasa al’adar riƙon amana da adalci a tsakanin gwamnati.”

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota