Shugaban Addinin Iran ya soki Amurka kan kisan bakaken fata

Shugaban Addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya soki lamirin kasar Amurka kan yadda ’yan sanda fararen fata suke ci gaba da kisan bakaken fata wadanda ba sa dauke da makamai, inda ya ce yanayin ya yi kama da halin kuncin da al’ummar Falasdinu ke fuskanta a yankin zirin Gaza. Jagoran addinin ya bayyana hakan […]

Shugaban Addinin Iran ya soki Amurka kan kisan bakaken fata
Shugaban Addinin Iran ya soki Amurka kan kisan bakaken fata

Shugaban Addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya soki lamirin kasar Amurka kan yadda ’yan sanda fararen fata suke ci gaba da kisan bakaken fata wadanda ba sa dauke da makamai, inda ya ce yanayin ya yi kama da halin kuncin da al’ummar Falasdinu ke fuskanta a yankin zirin Gaza.
Jagoran addinin ya bayyana hakan ne a shafin sada zumuntarsa na Twitter, ranar Lahadin da ta gabata, akan maudu’in da ke jan hankali kan muhimmancin rayukan bakaken fatan kasar Amurka wanda aka wa lakabi da #BlackLibesMatter. Khamenei ya dade yana amfani da wannan kafar wajen yin Allah-wadai da hukumomin kasar tun bayan kisan saurayin nan bakar fata Michael Brown, wanda wani jami’in dan sanda mai suna, Darren Wilson, ya kashe a ranar 9 ga watan Agustan bara, a garin Missouri. A rubutunsa a shafin na kwana- kwana nan, ya bayyana kasar Amurka da munafuka saboda yadda ta kwatanta waharhalun da masu zanga-zanga suka shiga a garin Missouri lokacin bukukuwan Kirsimeti da halin kuncin da Annabi Isa (AS) ya taba shiga.
 Hakazalika, a jajiberin Kirsimeti, Khamenei bayyana cewa: “Idan da Annabi Isa yana tare da mu a yau, zai jagoranci yaki da danniya kuma zai bai wa mutanen garin Ferguson da na zirin Gaza goyon bayansa.