Shugaban Afirka ta Kudu na fuskantar zargin almundahana
Almundahana da kudin gwamnati da suka kai Dala miliyan 20 (kimanin Naira biliyan 3 da miliyan 120) da ake zargin an kashe wajen gyara gidan Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ta tayar da muhawar kan halaccin tsayawarsa takara a zaben watan Mayu mai zuwa. Muhawarar ta zo ne a lokaci mai muhimmanci ga Shugaba […]
Almundahana da kudin gwamnati da suka kai Dala miliyan 20 (kimanin Naira biliyan 3 da miliyan 120) da ake zargin an kashe wajen gyara gidan Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ta tayar da muhawar kan halaccin tsayawarsa takara a zaben watan Mayu mai zuwa.
Muhawarar ta zo ne a lokaci mai muhimmanci ga Shugaba Zuma da jam’iyyarsa mai mulkin kasar ta ANC, wadda ta haye gadon mulki bayan tunkude mulkin mallaka a kasar kusan shekara 20 da suka gabata.
Jam’iyyun adawa na fatar yin amfani da wannan badakala wajen hada rikici tsakanin magoya bayan Jam’iyyar ANC da Shugaba Zuma, da karshen wa’adinsa na farko ke dab da zuwa karshe.
Shugaba Zuma ya ce jami’an tsaro na gwamnati ne ke gudanar da aikin gini a gidansa, kuma yunkurin ’yan adawa na samunsa da laifin yin almubazzaranci da kudin jama’a ba zai samu nasara ba, kamar yadda ya shaida wa jaridar gwamnatin kasar a ranar Litinin.
“Babu wani abin tuhuma,” jaridar The New Age ta ruwaito Zuma yana fadi a wajen wani kamfe a kusa da ofishin ’yan adawa a birnin Cape Town.
Ya ce “Za su iya nemana a ko’ina amma ba za su same ni ba, saboda ban aikata wani laifi ba.”
A ranar 19 ga Maris ne Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Afirka ta Kudu ta fitar da wani rahoto da ya ce Zuma ya amfana da wasu kudade ta hanyar da ba ta dace ba, kuma zai amayar da wasu kudade da ake zargin an inganta harkokin tsaro a gidansa da ke kauyen Nkandla. Wasu daga cikin gine-ginen da ake yi ba su da alaka da batun tsaro, ciki har da cibiyar baki da wurin kiwon kaji da kuma wurin da aka kebe wa shanu, kamar yadda rahoton ya nuna.
Babban Kwamitin ANC ya ce a tsaye yake wajen tabbatar da rikon amana, kuma ya lura da rahoton hukumar yaki da rashawar, amma akwai bukatar a bi bahasi ciki hard a samun rahoto daga bangaren Zuma.
Wani jigo a ANC Pallo Jordan ya rubuta a shafinsa na jaridar Business Day ind aya soki ministan da ke kula da aikin ginin, sannan ya ce ya kamata Zuma ya fahimci akwai babbar amana a kansa. Ya ce “Duk da cewa ya yi ayyukan sam barka a bangaren kiwon lafiya da ilimi da samar da ayyukan yi, mulkinsa cike yake da tabargaza.”