Shugaban Amurka Biden na neman tazarce
Biden na neman wa’adin mulki na biyu a zaben da za a gudanar a 2024
Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya bayyana aniyarsa ta neman wa’adi na biyu a karagar mulki.
Biden ya sanar da haka ne a safiyar Talata ta wani sakon bidiyo, wanda ya kawo karshen tantamar da ake yi game da sake tsayawarsa takara.
Hakan na nuna yiwuwar maimaita karon battar 2020 tsakaninsa da tsohon shugaban kasar, Donald Trump na Jam’iyyar Republican.
- ‘’Yan Matan Chibok’ 2 sun gudo daga hannun Boko Haram
- Yakin Sudan: ’Yan Najeriya miliyan 3 ne a Sudan —Abike
Kawo yanzu, Biden shi ne shugaban kasar Amurka mafi tsufa a lokacin da yake kan mulki a tarihi, lamarin da ake ta ce-ce-ku-ce a kai.
Sai dai a sanarwar tasa ta neman tazarce, ya jaddada cewa yawan shekarun ba zai hana shi kawo gagarumin cigaba ga Amurka ba.
A cewarsa, karin wa’adin zai ba shi damar cika alkawarinsa na dawo da martabar Amurka a idon duniya.
Ya bayyana cewa zaben kasar da za a gudanar a shekarar 2024 yaki ne domin ganin bayan tsattsauran ra’ayin jam’iyyar adawa ta Republican.
A cewarsa, “A lokacin da na fara tsayawa takara shekara hudu da suka gabata na bayyana cewa za mu yi dukkan mai yiwuwa wajen ceto kasar nan; kuma har yanzu muna kan yi.”
Idan ba a manta ba, tarzoma ta biyo bayan zaben 2020, inda magoya bayan tsohon shugaban kasar, Donald Trump suka yi tarzoma da kone-kone tare da keta hurumin majalisar dokokin kasar da zummar hana bayyana Biden a matsayin wanda ya yi nasara.
Sanarwar Biden ta ranar Talata na zuwa ne shekara hudu bayan bayyana aniyarsa ta takarar zaben 2020, wanda ya yi nasara.