Shugaban Amurka ya buƙaci ganawa ta musamman da Tinubu
Kai kaɗai ne shugaban da ya buƙaci ganawa da kai daga Afirka.
Shugaban Amurka Joe Biden ya aike da gayyata ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu domin gudanar da wata tattaunawa a tsakaninsu.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale, ya fitar ya ce Jakadan Shugaban Amurka na musamman, kuma Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Kasar, Ambasada Molly Phee ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci Shugaba Tinubu a fadarsa.
- Kada wanda ya kafa allunan taya ni murnar zama Minista – Wike
- Makiyayi mai shekara 15 ya guntule hannun manomi a Bauchi
Mista Phee ya shaida wa Tinubu cewa Shugaba Biden na buƙatar ganawa ta musamman da shi, a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a birnin New York cikin watan Satumba.
Jakadan na Amurka ya ce Tinubu ne kaɗai shugaban Afirka da shugaban Amurka ya karrama da gayyatar ganawa da shi.
Ya ƙara da cewa “Mun san akwai hanyoyin da za mu bi domin ƙarfafa zuba jarin Amurka a Najeriya, kuma muna son yin aiki kafaɗa-da-ƙafaɗa da kai domin cimma hakan, a wani ɓangare na inganta tattalin arzikin Najeriya da ma na Afirka.
“Muna yabawa da irin ƙoƙarin da kake yi wajen samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari.
“Saboda haka ne shugaba Joe Biden ke buƙatar ganawa da kai a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, kuma kai kaɗai ne shugaban da ya buƙaci ganawa da kai daga Afirka.
“Wannan kuma alama ce da ke nuna cewa ya yarda da nagartar shugabancinka,” in ji jakandan na Amurka.