Shugaban Amurka ya naɗa ’yan Najeriya 2 a matsayin mashawarta

Wata sanarwar fadar White House ce ta sanar da nadin nasu

Shugaban Amurka ya naɗa ’yan Najeriya 2 a matsayin mashawarta

Shugaban Amurka, Joe Biden, ya nada wasu Amurkawa biyu ’yan asalin Najeriya a matsayin masu ba shi shawara.

Mutanen da ya nada; Osagie Imasogie da Chineye Ogwumike, na cikin mutum 12 mambobin Majalisar Kula da Hulda da Kasashen Afirka a Ofishin Shugaban Kasar.

Bayanin nadin nasu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Amurka ta White House ta fitar a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, sauran mambobin majalisar mashawartan su ne Silvester Scott Beaman da zai jagoranci majalisar, sai Mimi E. Alemayehou da Rosalind Brewer da Viola Davis da kuma Helene D. Gayle.

Sauran su ne Patrick Hubert Gaspard da C.D. Glin da Osagie Imasogie da Almaz Negash da Chinenye Joy Ogwumike da Ham K. Serunjogi da kuma Kevin Young.

Mashawartan dai za su yi aiki ne daga tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025.

White House ta ce an kafa majalisar ce domin bunkasa alaka tsakanin gwamnatin Amurka da kasashen Afirka.

“Mambobin wannan majalisar sun kunshi mutanen da suka yi fice a harkokin gwamnati da wasanni da kirkira da kasuwanci da ilimi da ayyukan al’umma da kuma ayyukan addinai,” in ji sanarwar.