Shugaban Amurka zai gana da takwaransa na Rasha

A makon jiya ne, Shugaban kasar Rasha biladimri Putin ya sake lashe zaben kasar a matsayin wa’adi na hudu. Tun kafin a gudanar da zaben, kuri’ar jin ra’ayi da aka gudanar ta nuna cewa kusan kashi 70 na mutanen  Rasha suna goyon bayan Putin, wanda hakan ta sa aka kyautata zaton zai sake lashe zaben. […]

Shugaban Amurka zai gana da takwaransa na Rasha

A makon jiya ne, Shugaban kasar Rasha biladimri Putin ya sake lashe zaben kasar a matsayin wa’adi na hudu.

Tun kafin a gudanar da zaben, kuri’ar jin ra’ayi da aka gudanar ta nuna cewa kusan kashi 70 na mutanen  Rasha suna goyon bayan Putin, wanda hakan ta sa aka kyautata zaton zai sake lashe zaben.

Putin wanda shi ne Shugaban Rasha tun daga shekarar 2000, ya kara ne a wannan karo da abokan hamayya bakwai, daga cikinsu akwai attajirin kasar mai ra’ayin gurguzu Pabel Grudinin da tsohuwar ma’aikaciyar talabijin Ksenia Sobchak da bladmir Zhirinobsky.

Madugun ’yan adawar kasar Rasha Aledei Nabalny bai samu shiga zaben ba, sakamakon haramcin hakan da kotu ta yi masa bisa samunsa da laifin aikata almundahana, matakin da Nabalny ya bayyana a matsayin makircin siyasa. Kamar yadda gidan Rediyon Faransa Hausa ta ruwaito.

Jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben, Shugaban Amurka Donald Trump ya taya Putin murna duk da cewa masu ba shi shawara kan harkokin tsaro sun ja masa kunne.

Mista Trump ya mika masa sakon taya murnar ce a wata tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta wayar tarho, har suka amince za su gana a wani lokaci nan ba da jimawa ba.

“Watakila za mu gana nan ba da jimawa ba, domin mu tattauna kan batun makamai, mu tattauna kan gasar tara makamai,” inji shi. 

Mista Trump ya ce gasar kera makaman “Tana so wuce makadi da rawa,” amma Amurka, ba za ta kyale wata kasa ta mallaki ko kusa da abin da Amurka ta mallaka ba.” 

A tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta tarho, Shugaba Trump ya nanata muhimmancin kawar da makaman Nukiliya a yankin Koriya.

Wata sanarwa daga Rasha ta ce Shugaba Trump, da Putin sun yi magana kan muhimmancin aiki tare domin yaki da ta’addanci da takaita yaduwar makaman kare dangi da kuma hada kai ta fuskar tattalin arziki.