Shugaban Ansaru Khalid Albarnawi ya shiga hannu

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kama shugaban qungiyar Ansarul Islam fi Biladis Sudan da ta valle daga qungiyar Boko Haram, Khalid Albarnawi a garin Lakwaja da ke Jihar Kogi.Kafin vallewarsa daga qungiyar Boko Haram, ana xaukar Khalid Albarnawi, a matsayin Na’ibin Abubakar Shekau, shugaban Qungiyar Boko Haram.Qasar Amurka ta sanya ladan Dala miliyan biyar […]

Shugaban Ansaru Khalid Albarnawi ya shiga hannu
Shugaban Ansaru Khalid Albarnawi ya shiga hannu

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kama shugaban qungiyar Ansarul Islam fi Biladis Sudan da ta valle daga qungiyar Boko Haram, Khalid Albarnawi a garin Lakwaja da ke Jihar Kogi.
Kafin vallewarsa daga qungiyar Boko Haram, ana xaukar Khalid Albarnawi, a matsayin Na’ibin Abubakar Shekau, shugaban Qungiyar Boko Haram.
Qasar Amurka ta sanya ladan Dala miliyan biyar (kusan Naira biliyan xaya a kasuwar canji ta gwamnati ko Naira biliyan xaya da miliyan 600 a kasuwar bayan fage) ga duk wanda ya fallasa yadda za a kama Albarnawi, tare da bayyana shi daga cikin mutum uku ’yan Najeriya “da aka ayyana a matsayin ’yan ta’adda na duniya,” a shekarar 2012.
 Ansaru wadda ta valle daga Boko Haram ta yi qaurin suna wajen sace baqi ’yan qasashen waje tare da kashe su, tana da alaqa da qungiyar Alqa’ida a yankin Afirka ta Yamma. Ana zargin qungiyar da kai hari ga hedkwatar Hukumar Tsaro ta Qasa (DSS) da ke Abuja a shekarar 2012, inda ta sai waxanda ake tsare da su har mutum 40.
Daraktan Labarai na Sojin Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar ya tabbatar da kama Albarnawi ga Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, inda ya ce: “Jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara a ranar Juma’a a yaqin da suke yi da ta’addanci ta hanyar kama Khalid al-Barnawi, jagoran qungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru a Lakwaja. Yana daga cikin manyan ’yan ta’addan da muke nema.”
Wani rahoto a kafar sadarwa ta The Cable da ke Intanet ya ruwaito Ahmad Salkida wani xan jarida da ke iya samun bayania daga wasu shugabannin Boko Haram yana cewa jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama Albarnawi a Lakwaja da ke Jihar Kogi, kuma an taho da shi Abuja tun ranar Juma’ar da ta gabata.
Albarnawi mai shekara 47, sunansa na haqiqa shi ne Usman Umar Abubakar, kuma ya fito ne daga garin Biu da ke Jihar Borno kuma a cewar Salkida akwai bayanan da suke nuna  ya sasanta da Shugaban Boko Haram.
Rahotanni sun ce an horar da Albarnawai a qasar Aljeriya, kuma yana da qarfin faxa a ji a tsakanin ‘’yan ta’addan Najeriya, inda yake da alaqa da sauran qungiyoyin da ke da’awar jihadi a Afirka ta Arewa da Gabas ta Tsakiya.
A watan Yunin shekarar 2012 ne Amurka ta ayyana Albarnawi da Abubakar Shekau da Abubakar Adam Kambar a matsayin ’yan ta’adda. “Khalid Albarnawi da Abubakar Adam Kambar suna da alaqa da Boko Haram, kuma suna da dangantaka ta qut-da-qut da qungiyar Alqa’ida ta Yammacin Afirka,” inji sanarwar Amurka.
Al-Barnawi ya karvi shugabancin Ansaru ne bayan kashe Kambar a fafatawa da sojoji a wata mavoyarsu a Kano a watan Maris xin shekarar 2012.
Ministan Watsa Labari, Alhaji Lai Mohammed ya shaida wa AFP cewa: “Muna farin ciki kan wannan nasara (ta kame Albarnawi). Babbar nasara ce a yaqin da muke yi da ’yan ta’adda a qasar nan.”
Su Albarnawi sun valle daga Boko Haram ne saboda adawa da yawan dasa bama-bamai da kai hare-haren bindiga da take kan jama’a marasa qarfi, inda suka gwammace a riqa kai hari kan masu qarfi da kuma kan buqatun Turawan Yamma.  Kuma Kambar da Albarnawi tsofaffin na hannun daman shugaban Boko Haram ne marigayi Muhammad Yusuf.
Ana zargin Albarnawi da shirya sace wan xan Birtaniya da wani xan Italiya injiniyoyin gine-gine da suke aiki a Jihar Kebbi. Kuma Turawan biyu sun mutu a lokacin da sojoji na musamman ke qoqarin sako shi a cikin birnin Sakkwato a shekarar 2012.
Sannan shi ne ya tsara sace wani injiniyan gine-gine Bajamushe  mai suna Edgar Raupach a binrin Kano a shekarar 2012, inda shi ma ya mutu a lokacin da ake qoqarin ceto a wajen birnin Kano a shekarar.