Shugaban Boko Haram ya yi wa Sarkin Kano raddi
Shugaban kungiyar Ahlussunna lil da’awati wal jihad, wacce aka fi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da sabon bidiyo, inda ya mayar da raddi ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, game da jawabin da ya yi ga al’umma kwanakin baya, inda ya bukaci al’umma da su tashi su kare kansu daga hare-haren kungiyar.A […]
Shugaban kungiyar Ahlussunna lil da’awati wal jihad, wacce aka fi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da sabon bidiyo, inda ya mayar da raddi ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, game da jawabin da ya yi ga al’umma kwanakin baya, inda ya bukaci al’umma da su tashi su kare kansu daga hare-haren kungiyar.
A bidiyon mai tsawon kusan minti 20, Shekau ya yi jawabi na sama da minti 16 cikin harsunan Larabci da Hausa da kuma Kanuri, inda yake cewa sarkin ya makaro da wannan kira nasa.
Kamar yadda labari ya gabata, bayan kalaman na sarki ne dai aka kai hari mafi muni a jihar, a masallacin kofar gidansa, lokacin Sallar Juma’a a kawanakin baya, inda mutane sama da dari daya suka halaka, wasu kuma da dama suka samu raunuka. Wasu na ta’allaka want ton hari da cewa raddi ne na kai tsaye ga sarkin, yayim da kuma want ton bibiyon ke kara tabbatar da haka.
Baya ga raddin da ya yi wa sarkin, shugaban kuma ya bayyana sauran kungiyoyin addinin Musulunci a Najeriya da cewa ba su gudaar da Musulunci daidai, inda ya kira su da cewa kafirai ne.