Shugaban Brazil ya shiga tsaka-mai-wuya
Shugaban Brazil, Michel Temer ya shiga tsaka-mai- wuya bayan da hukumar ’yan sandan kasar ta bukaci mai shigar da kara na kasar ya gurfanar da Shugaban a gaban kotu tare da wadansu mutum 10 ciki kuwa har da ’yarsa. Ana zargin Shugaba Temer da mutanen 10 da laifin karbar cin hanci da rashawa da kuma […]
Shugaban Brazil, Michel Temer
Shugaban Brazil, Michel Temer ya shiga tsaka-mai- wuya bayan da hukumar ’yan sandan kasar ta bukaci mai shigar da kara na kasar ya gurfanar da Shugaban a gaban kotu tare da wadansu mutum 10 ciki kuwa har da ’yarsa.
Ana zargin Shugaba Temer da mutanen 10 da laifin karbar cin hanci da rashawa da kuma halatta kudaden haram. Hukumar ’Yan sandan Brazil ta kaddamar da wani bincike ne sama da shekara guda, domin tantance ko Shugaba Temer da ke kan karagar mulkin kasar tun daga shekarar 2016 na da hannu a cikin wata badakala ta cin hanci, inda ake zarginsa da karbar toshiyar baki kafin ya amince da wani kudiri a shekarar 2017 don zai taimaka wa ayyukan wasu kamfanonin tashoshin ruwa a kasar.
A halin yanzu dai kallo ya koma ga Ma’aikatar Shari’a, ko za ta shigar da kara kan Shugaban Kasar, ko za ta nemi a aiwatar da binciken kwakwaf, ko kuma ta yi watsi da batun. Bisa tsarin mulkin kasar ta Brazil dai, sai Majalisar Dokokin ta amince ne Kotun Kolin Kasar za ta iya aiwatar da nata bincike tare da gurfanar da Shugaban Kasar.