Shugaban Burkina Faso ya tsawaita wa’adin miƙa mulki zuwa shekara 5
An cimma wannan matsaya ne bayan ƙulla wata yarjejeniya a yau Asabar.
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, wanda ya hau karagar mulki a watan Satumban 2022 ta hanyar juyin mulki, zai tsawaita wa’adin mulkinsa na karin shekaru biyar.
Wannan na cikin wata yarjejeniya da mahalarta taron ƙasae suka amince da ita a ranar Asabar a babbann birnin ƙasar, Ouagadougou.
- Ba ni da hannu a dawowar Aminu Ado Bayero Kano — Ribadu
- Abin da ya sa na fara aikin DJ a Kano — Kyauta Dillaliya
“An saita tsawon lokacin miƙa mulki da watanni 60 daga ranar 2 ga watan mai kamawa, wato Yuli shekarar 2024,” in ji Kanar Moussa Diallo, shugaban kwamitin shirya waɗannan taruka.
Shugaba Traoré kuma zai iya kasancewa ɗan takara a zaɓukan ƙasar musaman neman kujerar shugaban ƙasa, ’yan majalisa da na ƙananan hukumomi waɗanda za a shirya don kawo ƙarshen miƙa mulki”, in ji Kanar Diallo.
Taron na ƙasar da aka shirya kammala shi a ranar Lahadinl, ya haɗa wakilan ƙungiyoyin farar hula da na tsaro da ma wakilai daga majalisar riƙon ƙwarya, amma mafi akasarin jam’iyyun siyasa sun ƙaurace wa taron.
A cikin sabuwar yarjejeniyar da Kyaftin Traoré ya rattaba wa hannu, an cire kujeru da aka saba ware wa jam’iyyun siyasa wanda ya shafi muƙaman wakilai na majalisar riƙon ƙwarya.
Burkina Faso, wacce ke fama da tashe-tashen hankula masu da’awar jihadi waɗanda suka yi sanadin mutuwar dubban mutane kusan shekara 10, ta fuskanci juyin mulkin soji guda biyu a 2022.
A cikin wannan tsari, an amince da wata yarjejeniya a tarukan ƙasa na farko, na samar da shugaban ƙasa, majalisar ministoci ƙarƙashin gwamnati, majalisar dokokin riƙon ƙwarya da kuma sanya lokacin miƙa mulki na watanni 21.
Don haka ya kamata a kawo ƙarshen wannan miƙa mulki a ranar 1 ga watan Yulin 2024, amma a lokuta da dama Kyaftin Traoré ya yi magana game da wahalar gudanar da zaɓe duba da yanayin tsaro a ƙasar.