Shugaban Chadi ga Shekau: Ka mika wuya ko mu kashe ka
Shugaban kasar Chadi Mista Idris Deby ya ce ko shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fito daga inda ya buya ko kuma sojojinsa su bi shi su kashe shi domin sun san inda yake boye. Mista Deby ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou, ya kai masa ziyara a Ndjamena, […]
Shugaban kasar Chadi Mista Idris Deby ya ce ko shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fito daga inda ya buya ko kuma sojojinsa su bi shi su kashe shi domin sun san inda yake boye.
Mista Deby ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou, ya kai masa ziyara a Ndjamena, babban birnin kasar a shekaranjiya Laraba.
Ya ce: “Mafi alheri ga Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya mika wuya; mun san inda yake. Idan bai mika wuya ba, makomarsa za ta zama iri daya da ta sauran mabiyansa.” Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito shugaban yana fada.
Idris Deby ya kara da cewa sun san cewa Shekau ya gudu daga garin Dikwa ne bayan sojojin Chadi sun fatattaki ’yan kungiyar daga garin, inda suka kashe sama da ’yan kungiyar 117 kuma aka kashe masa sojoji biyu a yayin ba-ta-kashin da suka yi ranar Talata. Ya ce ko Shekau ya fito ya yi saranda ko kuma su kashe shi kamar yadda suke yi wa mabiyansa.
Shugaba Idris Deby ya ce Chadi ba za ta daina barin wuta ba, har sai ta shafe kungiyar Boko Harm baki daya daga bayan kasa.
Rikicin Boko Haram wanda aka soma a Najeriya a shekarar 2009 a yanzu ya shiga makwabtan kasashe kamar Chadi da Kamaru da kuma Nijar, inda a watan Janairun kasashen uku suka tura da dakarunsu Najeriya domin dafa wa kasar ta yaki kungiyar.
Ana zargin Boko Haram da jawo mutuwar fiye da mutum dubu 15 tare da tilasta fiye da mutum miliyan daya yin gudun hijira daga muhallinsu tare da kai hare-hare a kauyuka da makarantu da kasuwanni da tashoshin mota da wuraren ibada.
Sau biyu sojojin Najeriya suke da’awar kashe Shekau, sai dai kuma daga baya sai ya fito a faifan bidiyo ya musanta haka.
Shugaba Deby ya ce: “Za mu ci nasarar yakin, mun sha alwashin shafe Boko Haram daga bayan kasa, sabanin abin da wasu kafafen watsa labarai ke tunani. Sojojin Chadi da na Nijar za su ci gaba da fafatawa don kawo karshen wannan matsoraciyar kungiya.”
A baya dai an zargi Shugaban na Chadi da tallafa wa mayakan Boko Haram ta hanyar ba su wurin samun horo a kasarsa, kuma ya rika zama kamar mai shiga tsakani a wani yunkurin tsagaita wuta da bai ci nasara a tsakanin kungiyar da gwamnatin Najeriya a bara.