Shugaban Chadi zai tsaya takara a karo na 5

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, wanda ya shafe  shekara 26 a kan mulki, ya ce zai sake tsayawa takara a karo na biyar a zaben da za a yi a watan Afrilu mai zuwa.Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato Shugaba Deby yana cewa zai takaita wa’adin mulki a kasar bayan an sake zabensa.A shekarar 1990 […]

Shugaban Chadi zai tsaya takara a karo na 5
Shugaban Chadi zai tsaya takara a karo na 5

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, wanda ya shafe  shekara 26 a kan mulki, ya ce zai sake tsayawa takara a karo na biyar a zaben da za a yi a watan Afrilu mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato Shugaba Deby yana cewa zai takaita wa’adin mulki a kasar bayan an sake zabensa.
A shekarar 1990 ne Shugaba Deby ya yi juyin-mulki, sannan daga bisani ya bukaci a rika gudanar da zabe a kasar.
A shekarar 2011 ne ya lashe zabensa na baya bayan nan.
Masu adawa da shugaban sun zarge shi da yin mulkin kama-karya, suna masu cewa ba a taba gudanar da sahihin zabe ba a kasar ba tun da ya karbe mulki.
Mista Deby, wanda dan-barandar kasar Faransa ne, na taka muhimmiyar rawa a yakin da ake yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Yammacin Afirka.
Wannan matakin na kara tsayawa takara yana zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen Burundi da Rwanda da kuma Kongo suke sauya kundin tsarin mulkin kasashensu don su samu damar tsayawa takara a karo fiye da sau biyu.