Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau

Nan gaba kaɗan za a fidda ranar da za a yi bikin naɗin sabon Magajin Rafin Zazzau.

Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau

Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau.

Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja.

Wakilinmu ya ruwaito cewa a yanzu ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada ne zai gaje shi a wannan kujera
ta hakimanci.

Farfesa Ango Abdullahi yana ɗaya daga cikin mazan jiya da suka yi ragowa a Nijeriya.

Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ɗaya ne daga cikin dattawan da al’umma suke buƙata musamman a wannan zamani.

Yana ɗaya daga cikin masu bayyana ra’ayin su a kowanne irin yanayi don jawo hankalin shugabanni da al’ummomi da nufin kyautata rayuwa.

Kazalika, Farfesa Ango Abdullahi shi ne na biyar a tarihin cikin jerin waɗanda suka riƙe muƙamin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tuni dai Masarautar Zazzau ta bayyana Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada wadda ƙani ne ga shi Farfesa Dahiru Ango Abdullahi a matsayin sabon Magajin Rafin Zazzau.

Sai dai masarautar ta ce zuwa nan gaba kaɗan za ta fidda ranar da za a yi bikin naɗin sabon Magajin Rafin Zazzau.