Shugaban DR Congo ya umarci dakarun MDD su fice daga kasar
Shugaba Felix Tshisekedi na Dimokuradiyyar Congo ya ba da umarnin ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga kasarsa
Shugaba Felix Tshisekedi na Dimokuradiyyar Congo ya ba da umarnin ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) daga kasarsa.
Tshisekedi ya sanar da haka ne a babban taron MDD, inda ya ce tun ya umarci gwamnatin kasarsa ta tabbatar ta gaggauta ficewar dakarun daga karshen wannan shekarar.
- Bazoum ya maka masu juyin mulki a Kotun ECOWAS
- NAJERIYA A YAU: Me Zai Faru Bayan Hukuncin Kotu Kan Zaɓen Kano?
A shekarar 2010 ne rundunar mai suna MONUSCo ta karbi aiki daga takwararata, da nufin samar da tsaro a gabashi kasar, inda kungiyoyi masu dauke da makamai ke yakar juna kan albarkatun kasa.
Sai dai muka a ’yan shekarun nan zaman dakarun a kasar na ci gaba da fuskantar adawa, saboda zargin gaza kare fararen hula, wanda hakan ya haifar da bore da zubar da jini a kasar.
A jawabinsa ga Babban Zauren MDD a ranar Laraba, Shugaban Tshisekedi, “Abin takaici ne a tsawon shekaru 25 rundunar wanzar da zaman lafiya da aka girke… ta kasa magance tarzoma da rikicin masu dauke da makamai.
“Shi ya sa… na umarci gwamnatin kasar ta fata tattaunawa da hukumomin MDD domin gaggauta ficewar dakarun rundunar MONUSCO… a watan Disamban 2023 maimakon Disamban 2024.”
Akalla mutum 40 ne aka kashe, aka jikkata wasu da dama a rikicin kin jinin MDD a birnin Goma da ke gabashin kasar a watan Agusta.
Gabanin haka, a watan Yulin 2022 irin haka ta yi ajalin mutum akalla 15, ciki har da dakarun rundunar guda uku.