Shugaban EFCC, Bawa, na ganawa da Tinubu a Aso Rock
Ana zataon tattaunawar na da nasaban da rikicin EFCC da DSS
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka yana ganawa da Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, a Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock da ke Abuja.
Ganawar na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan Tinubu ya umarci jami’an hukumar tsaro ta DSS su janye daga wani ofis mallakin EFCC da ke Ekoyi a Legas.
- Zargin Batanci: Kotu ta ba da umarnin a kamo Dokta Idris Dutsen Tanshi
- Tsohon Kakakin Buhari, Femi Adesina, ya samu sabon mukami
Bawa dai ya isa fadar ne wajen misalin karfe biyu da ’yan mintuna.
Kodayake ba a bayyana makasudin tattaunawar tasu ba, amma ana zaton ba za ta rasa nasaba da abin da ya faru tsakanin EFFC da DSS ba a Legas.
Rahotanni dai sun nuna cewa jami’an DSS dai sun toshe ofishin na EFCC da ke titin Awolowo Road a Ekoyin Jihae Legas a ranar Talata, inda suka hana jami’an yaki da rashawar shiga don yin aiki a ofishin nasu.
Sai dai daga bisani Shugaba Tinubu ya tsawatar, inda ya umarci DSS ta janye dakarunta daga ciki.
Lamarin dai na ranar Talata ya sake fitowa a fili irin rashin jituwar da ake samu tsakanin wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati a Najeriya.