Shugaban EFCC ya sha suka kan kama mawallafi a shafin Intanet
kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na masu fafutika a shafukan Intanet a kasar nan sun soki lamirin Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) Malam Ibrahim Magu saboda tsare wani mawallafi a shafin Intanet mai suna Abubakar Sidik Usman da aka fi sani da “Abusidik” a Intanet, bisa zarginsa da […]
kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na masu fafutika a shafukan Intanet a kasar nan sun soki lamirin Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) Malam Ibrahim Magu saboda tsare wani mawallafi a shafin Intanet mai suna Abubakar Sidik Usman da aka fi sani da “Abusidik” a Intanet, bisa zarginsa da aika sakan barazana.
Gidan rediyon BBC ya ruwaito cewa Hukumar EFCC tana zargin Abubakar Sidik Usman da laifin aika sakonnin barazana ne ta Intanet, abin da hukumar ta ce ya saba wa doka.
Sai dai a cewar BBC wasu rahotanni sun ce an kama Abubakar Sidik ne saboda ya rubuta wani labari a kan Shugaban Hukumar EFCC, Malam Ibrahim Magu, wanda bai yi wa EFCC dadi ba. An kama Sidik ne a gidansa da ke Kubwa, Abuja a ranar Litinin da ta gabata.
kungiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Kare Hakkin Jama’a (SERAP) ta zargi Hukumar EFCC da wuce gona da iri kan kamun Sidik Usman.
Wata kungiya mai suna Coalition of Human Rights Defenders (COHRD) ma ta fitar da sanarwa kan kama Abubakar Sidik din inda ta buga rahoton da ake zargin shi ne ya tunzura EFCC ta kama shi.
Usman, also known as Abusidiku, was arrested on the early hours of Monday 8th August, 2016 by operatibes of the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) purportedly ober a recent critical report he published against the Chairman of the Commission, Mr Ibrahim Magu.
Below is the article:
Ita ma kungiyar Matasa ta Jam’iyyar APC ta yi tir da kamun nasa, inda ta ce hakan yunkuri ne na yin kafar ungulu ga dokar fadin albakarcin baki. Hukumar ta bayar da belinsa inda aka sako shi washegari Talata.
A sakon da ya rubuta a shafinsa bayan sako shi, Sidik ya gode wa iyalai da lauyoyinsa da kungiyar Matasan APC da jam’iyyun siyasa da kungiyoyin kare hakkin jama’a da na masu amfani da Intanet kan yadda suka yi tsayuwar daka wajen kwato masa ’yancinsa.
Sidik yana daga cikin matasan da suka yi yaki sosai wajen samun nasarar Shugaba Buhari da Jam’iyyar APC ta amfani da Intanet, kuma ya yi alkawarin bayyana wa jama’a dalilan tsare shi da EFCC ta yi a nan gaba.