…Shugaban Ekuatorial Guinea ya raba wa talakawa dubu 40 tikitin shiga wasa
A shirye-shiryen da Ekuatrorial Guinea take yi na fara gasar cin kofin Afirka a gobe Asabar, Shugaban kasar Teodoro Obiang Ngueme ya raba wa talakawan kasar musamman marasa karfi tikitin shiga wasa su kimanin dubu 40 saboda su halarci wasan farko da kasar za ta yi da Kongo. An kiyasta shugaban ya kashe akalla Miliyan […]
A shirye-shiryen da Ekuatrorial Guinea take yi na fara gasar cin kofin Afirka a gobe Asabar, Shugaban kasar Teodoro Obiang Ngueme ya raba wa talakawan kasar musamman marasa karfi tikitin shiga wasa su kimanin dubu 40 saboda su halarci wasan farko da kasar za ta yi da Kongo.
An kiyasta shugaban ya kashe akalla Miliyan 20 kudin kasar (CFA) a sayen tikitin wanda ya yi daidai da Naira miliyan bakwai da doriya kudin Najeriya.
Sannan shugaban ya yi kira ga masu hannu da shuni da kamfanoni masu zaman kansu na kasar da su ma su yi koyi da shi wajen raba wa talakawan kyautar tikitin shiga wasa a lokacin da gasar ke gudana.
Shugaban ya ce ya yanke shawarar sai wa talakawa tikitin ne daga aljihunsa ba tare da taba asusun gwamnati ba, don shi ma ya bayar gudunmawarsa a gasar wajen ganin jama’ar kasar sun cika filin wasannin don kara wa gasar armashi.
Sannan shugaban ya ce ya bayar da umarnin a rage wa ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu lokacin tashi daga aiki a yayin gasar don su samu sukunin halartar filin wasannin don kashe kwarkwatar idanu.
Ya ce duk da yake Hukumar shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) ta amince wa kasar daukar nauyin gasar a kurarren lokaci bayan Maroko ta janye saboda tsoron barkewar cutar Ebola, kasar za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta samu nasarar duakar nauyin gasar.
Shugaban ya ce ko shakka babu Ekuatorial Guinea za ta samu bunkasar tattalin arziki saboda daukar nauyin gasar.