Shugaban Faransa ya aikewa Shugaban kamfanin Sanofi sammaci

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya aike da sakon sammaci ga shugaban babban kamfanin samar da magunguna na Sanofi bisa jawabin da ya yi akan riga-kafin cutar coronavirus. Fadar Elysee ta gayyaci shuganban kamfanin Paul Hudson biyo bayan wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijan din Bloomberg a Amurka inda ya bayyana cewa kasar […]

Shugaban Faransa ya aikewa Shugaban kamfanin Sanofi sammaci

Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya aike da sakon sammaci ga shugaban babban kamfanin samar da magunguna na Sanofi bisa jawabin da ya yi akan riga-kafin cutar coronavirus.

Fadar Elysee ta gayyaci shuganban kamfanin Paul Hudson biyo bayan wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijan din Bloomberg a Amurka inda ya bayyana cewa kasar ta Amurka za ta zamo kan gaba wurin cin moriyar riga-kafin idan aka samar dashi.

Gidan talabijan din ya rawaito Hudson yana cewa, Amurka za ta ci moriyar hakan ne saboda hannun jari da ta saka wurin daukar nauyin gudanar da binciken da zai samar da rigakafin.

Ya ce, hakan zai sa Amurka ta samu rigakafin makonni kamin a baiwa sauran bangarorin duniya.

Tun farko dai shugaba Emmanuel Macron ya bukaci cewa, duk wani riga-kafi da za a samar ya kamata a rarrabashi ba tare da nuna wariya ba wanda hakan ya sabawa bayanin na shugaban kamfanin na Sanofi ya yi.

A kokarin sassauta rashin fahimtar juna da hakan ka iya jawo wa, jagoran kamfanin, Serge Weinberg ya fadawa gidan talabijan na France 2 cewa duk da bayanin da Hudson ya yi, hakan yana nufin kasar Amurka za ta fara samun riga-kafin a cibiyoyin kamfanin da ke kasarta.

Kamfanin Sanofi dai yana da cibiyoyi biyu inda ake kokarin samar da riga-kafin wanda take gudanar da aikin tare da hadin gwiwar gwamnatin na Amurka.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya bayyana cewa ana sa ran samun riga-kafin a tsakiyar shekarar 2021.