Shugaban Gabon ya zama direban Messi
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya zama direban Messi a lokacin da shahararren dan kwallon FC Barcelona da Ajantina Lionel Messi ya kai ziyara kasar a ranar Asabar da ta wuce bayan shugaban ya gayyace shi bikin bude babban filin wasa mai suna Port-Gentil Stadium wanda za a yi amfani da shi a gasar cin […]

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya zama direban Messi a lokacin da shahararren dan kwallon FC Barcelona da Ajantina Lionel Messi ya kai ziyara kasar a ranar Asabar da ta wuce bayan shugaban ya gayyace shi bikin bude babban filin wasa mai suna Port-Gentil Stadium wanda za a yi amfani da shi a gasar cin kofin Afirka da zai gudana a kasar a shekarar 2017.
Bikin ya gudana ne a gari na biyu mafi girma a kasar watau Port-Gentil mai arzikin man fetur. Kuma dubban ’yan kallo ne suka yi tururuwar shiga filin wasan don yin ido da ido da Messi dan kwallon da suka dade suna son ganinsa a zahiri.
A filin wasan ne Lionel Messi ya rika daukar hoto da jama’a da dama, inda daga bisani ya shiga wata motar alfarma da shugaban ya ware masa kuma shufaban kasar ne da kansa ya tuka shi ba tare da umartar wani ya yi hakan ba. Shugaban ya ce ya yi haka ne don nuna irin soyayyar da yake yi wa Messi da kuma jin dadin cika alkawarin da ya yi musu na ziyartar kasar a karon farko.
Shugaba Ali Bongo ya ce a lokacin da ya kai ziyara kulob din FC Barcelona kimanin shekaru biyu da suka wuce ne ya gayyaci Lionel Messi zuwa Gabon inda dan kwallon ya tabbatar masa zai ziyarci Gabon din, to ga shi yau dan kwallon ya cika alkawarinsa kuma hakan ce ta sa na yanke shawarar na tuka shi a mota da kaina, ba tare da sanya wani ba, don nuna farin ciki.
A nasa bangaren Lionel Messi, ya bayyana farin cikinsa a kan irin kyakkyawar tarbar da Shugaban da kuma mutanen Gabon suka yi masa. Ya yaba wa magoya bayansa a kan yadda suka rika murna suna sowa a lokacin da suka yi arba da shi a filin wasan.
Idan za a tuna Gabon ce tare da hadin gwiwar Ekuatorial Guinea suka dauki nauyin gasar cin kofin Afirka a shekarar 2012 a matsayin hadin gwiwa. A wannan shekarar ce kuma Ekuatorial Guinea ta dauki nauyin gasar bayan kasar Maroko ta janye. Sannan a shekarar 2017 ce ake sa ran Gabon za ta sake daukar nauyin gasar ita kadai ba tare da wani hadin gwiwa ba.
Tuni Lionel Messi ya bar kasar ya koma gida.