Shugaban Gambiya ya koma gida bayan yunkurin juyin mulki

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasar Gambiya Yayha Jammeh ya koma gida bayan wani yunkurin juyin mulki da bai samu nasara ba, lokacin da shugaban ya kai ziyara kasar Faransa.A ranar Talata ne dai masu aiko da rahotanni suka bayyana cewa an ji karar harbe-harbe a fadar shugaban kasar da ke Banjul, babban birnin kasar, […]

Shugaban Gambiya ya koma gida bayan yunkurin juyin mulki

A shekaranjiya Laraba ne Shugaban kasar Gambiya Yayha Jammeh ya koma gida bayan wani yunkurin juyin mulki da bai samu nasara ba, lokacin da shugaban ya kai ziyara kasar Faransa.
A ranar Talata ne dai masu aiko da rahotanni suka bayyana cewa an ji karar harbe-harbe a fadar shugaban kasar da ke Banjul, babban birnin kasar, amma mahukunta sun ce an dakile yunkurin.Kodayake, Shugaba Jammeh ya ce ne kasarsa ta fuskanci wani kutse daga makwabciyarta kasar Senegal. Sai dai wani jami’i ya ce komai ya koma daidai a kasar. Kodayake, wani gidan rediyo mai goyon bayan ’yan adawa ya ce harkokin kasuwanci sun tsaya cak a kasar. Kuma an ruwaito cewa jama’a sun kaurace wa birnin Banjul shekaranjiya Laraba.
Shugaba Jammeh ya karbe mulki ne a karamar kasar da ke yankin Yammacin Afirka a shekarar 1994 kuma ana masa zargin wanda ba ya lamuntar ’yan adawa. Ya lashe zabe akai-akai tun bayan darewarsa karagar mulkin, sai dai masu sukarsa sun sha zarginsa da tafka magudi.