Shugaban Ghana ya jagoranci shirin tsaftace muhalli

Gwamnatin kasar Ghana ta kaddamar da shirin tsaftace muhalli, bayan da aka samu abarkewar annobar kwalara, ala’amarin da ya haifar da asarar rayuka. Ganin haka Shugaban kasa da mataimakinsa suka fito don nuna wa al’umma muhimmancin tsaftas, inda suka rika kwashe shara tare da jama’a. Bisa la’akari da munin lamarin ne, gwamnati ta gabatar da […]

Shugaban Ghana ya jagoranci shirin tsaftace muhalli
Shugaban Ghana ya jagoranci shirin tsaftace muhalli

Gwamnatin kasar Ghana ta kaddamar da shirin tsaftace muhalli, bayan da aka samu abarkewar annobar kwalara, ala’amarin da ya haifar da asarar rayuka. Ganin haka Shugaban kasa da mataimakinsa suka fito don nuna wa al’umma muhimmancin tsaftas, inda suka rika kwashe shara tare da jama’a.

Bisa la’akari da munin lamarin ne, gwamnati ta gabatar da gangamin magance matsalar shara cikin kasar, har ta kai ga shugaban kasa da kansa John Dramani Mahama da mataimakinsa Amissah Arthur sun fito an yi shara tare da su.
daukar wannan mataki ya zama dole, saboda haka ta tsayar da ranar tsafta,inda kowa zai daina duk wani abin da yake yi tun safe a fito a share unguwani.
Ranar farko da aka soma gudanar da wannan shiri, ita ce Asabar daya ga watan Nuwamba, kuma al’umma sun fito haikan don yin shara.
Shugaban kasa da kansa ya yi tattaki har Jihar bolta,inda ya shige cikin al’ummar yankin suka yi aikin tsaftace muhallinsu. A cikin Jawabinsa ga al’ummar da suka hada da sarakuna da sauran masu fada aji, ya bukaci ’yan Ghana su tabbatar da tsaftar muhallinsu.
Ya ce, akwai bukatar wayar da kan al’umma game da muhimanci yaki da cutar kwalara, wacce ta cinye rayuka da yawa a fadin kasar. Ya ce duk da mutuwar da ake yi, halayen mutane bai canza ba game da tsaftar jiki da kuma kewayen gidajensu .
“Za ka ga mutane na yin bayan gari a filin Allah da cikin kwatoci, yayin da shara kuma ta cike mana kasuwanni,” inji shi.
Ya ce, ya yi imani da cewa, fitowarsa za ta kara wa al’umma himma, inda jama’a suka rungumi yadda aka kaddamar da shirin da muhimmanci don tsabtace muhallinsu.
A nan birnin Accra mataimakin shugaban kasa Amissah Arthur, kuma ya yi jawabi ga manema labarai bayan kaddamar da shirin, inda ya jaddada bukatar jama’a su tabbatar da tsabtar wurin zamansu da jikinsu da muhallinsu.Ya ce idan jama’a suka rika tsaftace kewayen unguwaninsu, ta yadda hakan zai taimaka wa hukumomi wajen gudanar da ayyukansu.