Shugaban Ghana ya kaddamar da bai wa dalibai takalma kyauta
A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya kaddamar da wani shirin raba wa yara ’yan makarantar firamare takalma kyau, wadanda aka kera a kasar a unguwanin marasa galihu. An gabatar da shirin ne a wata unguwar Ada Foah cikin da ke cikin birnin Accra. Takalman da aka fi […]
A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya kaddamar da wani shirin raba wa yara ’yan makarantar firamare takalma kyau, wadanda aka kera a kasar a unguwanin marasa galihu.
An gabatar da shirin ne a wata unguwar Ada Foah cikin da ke cikin birnin Accra. Takalman da aka fi saninsu da sunan Achimota Sandals, wata masana’anta mai suna, Defence Industrial Holding Corporation, wadda aka sani da Kumasi Shoe Factory karkashin Ghana Industrial Holding Corporation (GIHOC) ne suka kera su.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki ga majalisan dokoki a farko bana, Shugaba Mahama ya yi alkawarin zai raba wa ’yan makaranta da ke kananan makarantu takalma dubu 10 kerar Ghana kyauta a matsayin wani bangare na shirn inganta yin karatu.
“Na yanke shawarar raba takalma ne lokacin da muke raba wa tufafin makaranta wato Uniforms. Bayan mun fahimci cewa dimbin daliban makarantar ba su da takalma sanyawa, ”inji shi.
Daga nan ya yi fatan takalma za su rage wa iyaye yawan kudin da suke kashewa wajen ilimin ’ya’yan su.
Ya c igaba da cewa ma’aikatar ilimin kasar ta fara rabon na’ura Kwamfuta dubu 20 ga makarantu.
Har ila yau, akwai wasu karin rigunan makaranta dubu 500 da littafan rubutu milliyan 15 da za a raba kyauta ga daliban a bana.
Dangane da manyan makarantun sakandare, Shugaba Mahama, ya ce gwamnatinsa ta yi nisa wurin gina guda 50 a zangon farko, kuma an kama haramar gina wasu 23.