Shugaban gwamnonin Najeriya ya kamu da COVID-19

Fayemi ya zama na bakwai a cikin gwamnonin Najeriya da suka kamu da cutar.

Shugaban gwamnonin Najeriya ya kamu da COVID-19

Shugaban Zauren Majalisar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti

Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya sanar da kamuwarsa da cutar Covid-19.

Fayemi wanda shi ne shugaban Kuniygar Gwamnonin Najeriya (NFG), ya zama na bakwai a cikin gwamnonin Najeriya da suka kamu da cutar.

Sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba ta ce “Na yi gwajin COVID-19 dina na uku jiya (Talata) kuma sakamakon ya nuna ina dauke da cutar.

“Ina cikin koshin lafiya amma na riga na killace kaina a gida domin likitoci su kula da lafiyata.

“Na hannata muhimman ayyukana ga mataimkina amma zan ci gaba da yin sauran ayyuka na yau da kullum daga gida”, inji shi

Gwamnan Kaduna Nasiar El-Rufai ne gwamnan Najeriya da ya fara kamuwa da cutar a watan Maris kafin daga bisani takwaransa na Bauchi Bala Mohammed ya harbu.

Sauran su ne Ifeanyi Okowa na jihar Delta, Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, sai David Umahi na jihar Ebonyi da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo,

Sia dai kuma dukkan sauran gwamnonin da kamu da cutar sun warke.