Shugaban Habasha ya yi murabus
A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Habasha, Mulatu Teshome ya mika takardar yin murabus daga mukaminsa ga Majalisar Dokokin Kasar. Teshome wanda yake rike da ragamar Shugaban Kasar tun shekarar 2013, ya mika takardar murabus din ce, inda majalisun kasar suka ce za su sanya ranar da za su yi nazari a kan bukatarsa. Majalisun ne […]
Tsohon Shugaban Habasha, Mulatu Teshome
A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Habasha, Mulatu Teshome ya mika takardar yin murabus daga mukaminsa ga Majalisar Dokokin Kasar. Teshome wanda yake rike da ragamar Shugaban Kasar tun shekarar 2013, ya mika takardar murabus din ce, inda majalisun kasar suka ce za su sanya ranar da za su yi nazari a kan bukatarsa.
Majalisun ne suke da hurumin ayyana wanda zai maye gurbin shugaban, kuma a zaman Majalisar Dokokin kasar a jiya Alhamis, ta amince da nada Misis Sahle-wuk Zewade don ta maye gurbin Teshome a matsayin Shugaban Kasa.
Teshome mai shekara 63 ya rike mukamai masu yawa a kasar Habasha, ciki har da Mataimakin Ministan Tattalin arziki da ci gaban kasa, sannan ya kuma rike Ministan Noma, ya kuma taba zama Kakakin Gwamnatin Tarayyar Kasar.