Shugaban Haiti ya sauka daga mulki ba tare da zaben magajinsa ba
Shugaban kasar Haiti Mista Michel Martelly ya sauka daga kujerar mulkin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bukace shi, bayan cikar wa’adin mulkinsa na shekara 5 ba tare da an zabi wanda zai maye gurbinsa ba, bayan an dage zaben kasar sau biyu bisa zargin magudin zabe […]
Shugaban kasar Haiti Mista Michel Martelly ya sauka daga kujerar mulkin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bukace shi, bayan cikar wa’adin mulkinsa na shekara 5 ba tare da an zabi wanda zai maye gurbinsa ba, bayan an dage zaben kasar sau biyu bisa zargin magudin zabe a watan Oktoba da Disamban bara.
Gabanin saukar Shugaba Mitchel Martelly, wanda tsohon mawaki da kade-kaden Turawa ne, ya shaida wa wakilan Majalisar Dokokin kasar Haiti a birnin Port-Au-Prince cewa, zai sauka daga mulkin ne don ya bayar da tasa gudunmawar wajen tabbatar da daidaiton kundin tsarin mulkkin kasarsu.
Shugaban sai ya mika ragamar mulkin kasar Majalisar Dokokin wadda ke da tsananin tsaro. Wakilan Majalisar ne za su zabi wanda za a ba shi rikon kwaryar mulki kafin lokacin da ya kamata a yi zaben Shugaban kasar, bayan an cimma wata yarjejeniya awoyi 22 kafin Martelly ya sauka daga mukaminsa.
A karkashin yarjejeniyar, majalisar za ta zabi shugaban riko wanda zai yi mulki na kwana 120, inda za a tabbatar da shi a matsayin Firayi Minista.
Kuma za a sake gudanar da zabubbuka a ranar 24 ga Afrilu mai zuwa, yayin da ake sa ran za a rantsar da wanda ya yi nasara a ranar 14 ga Mayu.
Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya Mista Ban Ki-moon ya yi kiran a kwantar da hankali a kasar a ranar Litinin da ta gabata, inda ya tabbatar wa kasar kudirin majalisar na “bayar da cikakken goyon baya ga al’ummar Haiti a kokarinsu na cimma burinsun na samun gwamnatin dimokuradiyya,” inji shi.