Shugaban Hukumar Alhazan Jihar Kaduna ya sauka daga mukaminsa

Ranar Talatar da ta wuce Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, Malam Tahir Umar Tahir ya sauka daga mukaminsa, sakamakon nada shi da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi a maysayin mai ba shi shawara a kan harkokin Addinin Musulunci da kula da masallacin fadarsa da ke Abuja.Da yake jawabi ga manema […]

Shugaban Hukumar Alhazan Jihar Kaduna ya sauka daga mukaminsa

n Gwamna Ramalan Yero na Jihar KadunaRanar Talatar da ta wuce Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, Malam Tahir Umar Tahir ya sauka daga mukaminsa, sakamakon nada shi da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi a maysayin mai ba shi shawara a kan harkokin Addinin Musulunci da kula da masallacin fadarsa da ke Abuja.
Da yake jawabi ga manema labarai kafin ya mika ragamar shugabancin hukumar ga sabon shugabanta, Malam Tahir ya gode wa Gwamnan Jihar Mukhtar Ramalan Yero bisa damar da ya ba shi ya shugabanci hukumar. “Komai ya yi farko zai yi karshe, a yau Talata 13 ga Agusta na sauka daga kan wannan mukami nawa. Na kuma sauka ne saboda sabon mukamin da Allah Ya ba ni a matsayin mai ba Shugaban kasa shawara a kan Harkokin Addinin Musulunci da kula da Masallacin Fadar Shugaban kasa. Wannan abu da ya zo min dole ne in nemi zabi, saboda haka ni da shugabannina, Mai girma mataimakin Shugaban kasa da Mai girma Gwamna da sauran iyaye wadanda ake tattaunawa da su mun duba al’amarin inda muka ga cewa a zabi zuwa a taimaka wa addini a kasar nan baki daya ya fi a zauna a Kaduna,” inji shi.
Ya ce, “Wadanda ke ta suka da zargin na ki sauka daga mukamin saboda in ci gida biyu to, yau na sauka saboda haka sai a rufe shafina. Ina kuma fatan su sani cewa Allah ne ke ba da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya so.”
Ya roki gafarar ma’aikatar hukumar idan ya saba wa wani daga cikinsu a lokacin shugabancinsa.
Daga bisani ya mika ragamar shugabancin hukumar ga Daraktan Tsare-Tsare na Hukumar, Malam Kabiru kasim a matsayin Mukaddashin Babban Sakataren Hukumar.
A jawabin Mukaddashin Babban Sakataren Hukumar cikin hawaye ya roki ma’aikatan hukumar ne su taimaka masa domin sauke wannan nauyi da aka dora masa.
“Wannan ba abin murna ba ne idan muka yi la’akari da kalubalen da ke cikin wannan aiki, saboda haka ina rokonku ku taimaka mana da addu’a. Ina kuma rokon goyon bayanku domin ba zan iya aikin ni kadai ba,” inji shi.