…Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tunisiya ya yi murabus a Hukumar CAF saboda zargin an yi wa kasarsa magudi

A ranar Litinin da ta wuce ne Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tunisiya Wadie Jary ya bayyana cewa ya ajiye aiki da Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ganin yadda aka yi wa kasarsa coge a wasan Kwata-Fainal inda Ekuatorial Guinea ta doke ta Tunisiya da ci 2-1 a wasan. A wasan da kasashen […]

…Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tunisiya ya yi murabus a Hukumar CAF saboda zargin an yi wa kasarsa magudi
…Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tunisiya ya yi murabus a Hukumar CAF saboda zargin an yi wa kasarsa magudi

A ranar Litinin da ta wuce ne Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tunisiya Wadie Jary ya bayyana cewa ya ajiye aiki da Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ganin yadda aka yi wa kasarsa coge a wasan Kwata-Fainal inda Ekuatorial Guinea ta doke ta Tunisiya da ci 2-1 a wasan.

A wasan da kasashen biyu suka yi a ranar Asabar da ta wuce ne, a lokacin wasa na 1-1 sai alkalin wasa ya ba Ekuatorial Guinea bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti) ana gab da tashi wasa bayan an kara wa’adin minti talatin (edtra-time) da hakan ya sa aka fitar da Tunisiya daga gasar.
Jim kadan bayan an tashi wasan ne, sai Kocin Tunisiya George Leekens ya zargi alkalin wasan da yi musu magudi don ya farantawa mai masaukin baki Ekuatorial Guinea rai. Hakan ta sa kasar ta fitar da sanarwar yin murabus din Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tunisiya Wadie Jary da memba ne a Kwamitin shirya gasar cin kofin Afirka da ke gudana a halin yanzu.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Ekuatorial Guinea take samun bugun fanari a gasar, al’amarin da ya sa ta rika samun nasara kuma har ta kai wannan mataki ba a yi waje da ita a gasar ba.