Shugaban hukumar leken asirin Isra’ila ya yi murabus
Manjo- Janar Aharon Haliva, shi ne babban hafsan soji na farko da ya yi murabus bayan caccakar da ya fuskanta kan gagarumin harin
Shugaban hukumar leken asiri ta kasar Isra’ila, Manjo-Janar Aharon Haliva, ya yi murabus saboda harin da ba da taba ganin irinsa ba da kungiyar Hamas ta kai wa kasar.
Manjo- Janar Aharon Haliva, shi ne babban hafsan soji na farko da ya yi murabus bayan caccakar da ya fuskanta kan gagarumin harin na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
A takardarsa ta barin aiki, Haliva ya ce ya dauki laifin kasa dakile harin da ya Hamas ta tsallaka katangar Iyaka da ma duk matakan tsaron Isra’ila har ta kai harin da aka kashe mutane 1,139, ta kuma yi awon gaba da wasu darruruwa zuwa Gaza, inda ta yi garkuwa da su.
Ana ganin hakan zai bude kofa da manyan jami’an sojin kasar za su dauki laifin harin da ake ganin Hamas ta kada hantar Isra’ila fiye da kowane lokaci.