Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri ya yi murabus
Shugaban bai bayyana dalilinsa na ajiye aikin nasa ba.
Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Ya bayyana haka ne ga maneman a fadar shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan ganawarsa da shugaba Tinubu.
- Ambaliya: Mutum 6 sun rasu, 2,000 sun rasa muhalli a Adamawa
- Gobara: NEMA ta raba kayan abinci a Zamfara da Sakkwato
Ya gode wa shugaba Tinubu bisa ba shi damar ci gaba da jagorantar hukumar bayan ya zama shugaban ƙasa.
Ya ce ya je fadar shugaban ƙasar ne domin ganawa da shi, don yi masa bayanai kamar yadda ya saba a ko yaushe, wanda daga nan ne ya ajiye aikinsa.
“Bayan na yi masa jawabi, na kuma gabatar masa da takardar ajiye aikina, kuma shugaban ƙasar ya karɓe ta tare da amincewa da ita.
“Na gode masa bisa damar sa ya ba ni na yi wa Najeriya hidima, kuma ya ƙara tsawaita lokacin zuwa watanni 15…”
To sai dai bai yi cikakken bayani kan dalilinsa na ajiye aikin a daidai wannan lokacin ba.
Ya kuma ce yana alfahari bisa aikin da ya yi da shugabannin ƙasar har guda biyu.
A watan Janairun 2018 ne dai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar, bayan korar tsohon shugaban hukumar Ayo Oke, bisa zargin almundahana.
Tsohon mai shekara 71, ya yi ritaya daga aiki a Jihar Katsina, tare da shiga sashen tsaro na ma’aikatar harkokin wajen Najeriya a 1993.
A shekarar 2015, an naɗa shi babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa (SSAP) kan hulɗa da ƙasashen duniya da kuma harkokin waje.