Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Bauchi (BASIEC), Ahmed Makama Hardawa, ya rasu.

Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu

Ahmad Makama Hardawa

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Bauchi (BASIEC), Ahmed Makama Hardawa, ya rasu.

Marigayin ya rasu ne ranar Talata a Abuja, bayan ya yi fama da gajeruwar jinya.

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Gidado, ya bayyana kaduwa da alhininsa kan rasuwar, inda ya bayyana rashin marigayin a matsayin babban rashi ga jihar da ma kasa baki daya.

Sanarwar ta kuma ce, “Za a yi kewar kwarewarsa a wannan lokacin mai matukar muhimmanci ga Dimokuradiyyarmu. Dattijo ne da ya sadaukar da rayuwarsa a aikin gwamnati da hidimta wa Jihar Bauchi da ma kasa baki daya.

“Ya taba zama Kwamishinan Hukumar Zabe ta Kasa a jihohin Taraba da Nasarawa, kuma ya yi aikinsa cikin kamanta gaskiya, rikon amana da kuma jajircewa.

“A matsayinsa na shugaban hukumar BASIEC, Hardaway a taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantattun zabuka. Irin jajircewarsa wajen ganin an yi komai a bisa ka’ida ya jawo masa kima a idanun abokan aikinsa ’yan siyasa da ma sauran jama’a,” in ji Gwamnan.

Daga nan sai ya yi addu’a Allah ya yi wa mamaci gafara sannan y aba iyalansa hakurin jure rashinsa.

Sanarwar ta kuma ce za a yi jana’izar marigayin a a fadar Sarkin Bauchi da misalign karfe 5:00 na yammacin Laraba.