Shugaban Iran ya nemi Fafaroma ya yi masa addu’a
Shugaban Jamhuriyyar Musulunci ta Iran, Hassan Rouhani ya gana da Fafaroma Francis a fadarsa da ke batican inda ya bukaci Fafaroma ya yi masa addu’a a daidai lokacin da yake fara ziyarar kasashen Turai. Rouhani ya bukaci shugaban na mabiya cocin Katolika na duniya ya yi masa addu’ar ce lokacin da ya isa birnin Roma […]
Shugaban Jamhuriyyar Musulunci ta Iran, Hassan Rouhani ya gana da Fafaroma Francis a fadarsa da ke batican inda ya bukaci Fafaroma ya yi masa addu’a a daidai lokacin da yake fara ziyarar kasashen Turai. Rouhani ya bukaci shugaban na mabiya cocin Katolika na duniya ya yi masa addu’ar ce lokacin da ya isa birnin Roma na kasar Italiya don fara ziyarar kasasshen Yammacin duniya. Shugaban wanda suka yi musayar kyauta da Fafaroma Francis ya bukaci Fafaroma ya yi masa addu’ar ce a ganawar kashin kai da suka yi.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa Shugaba Rouhani ya ba wa Fafaroma Francis wani kafet mai girman sentimita 80 (inci 32) da fadin mita 1.2 ko kafa hudu inda ya bayyana cewa an yi kafet din ne da hannu a birni mai tsarki na kum.
Fafaroma ya yi kasake yana sauraren Rouhani lokacin da yake duba wani littafi mai dauke da zanen hotuna da aka wallafa a Iran. Fafaroma Francis ya yi musabaha da Rouhani wanda yake kokarin dawo da Iran cikin kasashen duniya tare da mayar da ita mai fada a ji a yankin Gabas ta Tsakiya bayan kulla yarjejeniyar dakatar da aikin makamin nukiliya na Iran da ta cimma da kasasahen Yamma.
Fafaroma Francis ya ba Shugaba Rouhani kyautar wani sassaken zane na Waliyyi Martin da aka yi da ruwan zinari, kyautar da Fafaroma ya bayyana da cewa alama ce ta nuna ’yan uwantaka.
A ranar Litinin ne Shugaba Rouhani ya fara ziyarar kasahen Turai tare da yada zango a kasar Italiya domin fara harkokin kasuwanci gadan-gadan da Turai bayan janye wa Iran din takunkumi.