Shugaban Izala ya kammala biyan kudin masallaci

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Kano, Sheikh Dokta Abdullahi Saleh Pakistan ya kammala biyan ragowar Naira dubu  400 kudin ginin Masallachin Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da ke Unguwar Sabuwar Gandu da ya ranci Naira dubu 900 daga asusun ginin masallacin. Biyan kudin ya biyo […]

Shugaban Izala ya kammala biyan kudin masallaci

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Kano, Sheikh Dokta Abdullahi Saleh Pakistan ya kammala biyan ragowar Naira dubu  400 kudin ginin Masallachin Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da ke Unguwar Sabuwar Gandu da ya ranci Naira dubu 900 daga asusun ginin masallacin.

Biyan kudin ya biyo bayan umarnin Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Lemo karkashin jagorancin Mai shari’a Ibrahim Bala Ibrahim, wanda tun a watan Yuli ya bai wa shugaban umarnin biyan kudin.

A ranar 26 ga Oktoban da ya gabata ne Sheikh Pakistan ya biya Naira dubu 500 tare da alkawarin biyan sauran kudin.

Tunda farko wani mutum ne mai suna Ahmad Muhammad ya shigar da kara, inda ya nemi kotun ta tilasta wa Shugaban Izalar na Kano ya biya Naira dubu 900 da ya karba daga hannunsa, mallakar asusun ginin masallacin.

Mai karar ya shaida wa kotun cewa Dokta Abdullahi Pakistan ya karbi rancen Naira miliyan daya da dubu 300 daga asusun ginin masallacin sai dai ya biya Naira dubu 400 daga ciki yayin da ya gaza biyan sauran kudin.

A cewar mai karar, ya yi iyakar kokarinsa a kan Shugaban na Izala, ya biya kudin amma abin ya faskara, inda hakan ya sa ya yi kararsa a gaban kotu don ta tilasta masa ya mayar  da kudin.

Tuni aka mika kudin ga Kwamitin Ginin Masallacin Juma’ar, inda kwamitin ya mika ga Kungiyar Ci gaban Sabuwar Gandu.