Shugaban Izala ya nemi gwamnatin Yobe ta fi ba da karfi ga inganta rayuwar jama’a

Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Yobe kuma Babban Limamin Pomfamari da ke Damaturu Ustaz Ibarhim Muhammad Damaturu ya shawarci gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’umma jihar maimakon gina hanyoyi da gine-gine da sauran abubuwan kyale-kyale, musamman a halin da ake ciki na fatara da […]

Shugaban Izala ya nemi gwamnatin Yobe ta fi ba da karfi ga inganta rayuwar jama’a

n Gwmnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim GaidamShugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Yobe kuma Babban Limamin Pomfamari da ke Damaturu Ustaz Ibarhim Muhammad Damaturu ya shawarci gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’umma jihar maimakon gina hanyoyi da gine-gine da sauran abubuwan kyale-kyale, musamman a halin da ake ciki na fatara da talauci da ya fi addabar al’umma sakamakon tabarbarewar tsaro na tsawon shekara biyu.
Malam Ibrahim Damaturu ya bayyana haka ne a tattaunawarsu da Aminiya a Damaturu, inda ya ce kasancewar an yi fama da matsaloli da yawa a jihar a tsawon shekara biyu inda sanadin haka mutane da yawa suka rasa rayukansu wasu suka samu karayar arziki mabukata suka karu yayin a jihar wadda ke cikin jihohin da suke a baya a fannin tattalin arziki, ya kamata mahukuntan jihar su karfafa bangaren taimaka wa jama’a da abinci da sutura da muhalli da jarin gudanar da sana’a da kasuwanci.
Ya ce ya san mahukuntan jihar da gwamnatoci da daidaikun jama’a suna bakin kokarinsu wajen tallafa wa jama’a, to, amma abin bai isa saboda don halin da ake ciki ya wuce kwatantawa sai wanda ya gani da idonsa. “Inganta rayuwar dan Adam shi ke gaba da gine-gine, saboda mutum ya fi komai daraja saboda Allah Ya halicci duniya ne dominsa. Kaga ashe Allah da kanSa Ya damu da shi fiye da kyale-kyalen duniya,” inji shi.
Ya ce in ba a inganta rayuwar al’umma, to, duk aikin da aka yi ba zai yi tasiri ba, don makaranta ake so talaka ya kai ’ya’yansa idan yana fama da yunwa da talauci, karatun ba zai yiwu ba.
Game da harkokin tsaro kuwa shugaban ya jinjina wa gwamnatin jihar da jami’an tsaron da ke kula da dawo da zaman lafiyar a jihar kan namijin kokarin da suke yi na samar da tsaro mai inganci, “Yadda jama’a da yawa suka halarci Idin karamar Sallah ya nuna an samu ingantuwar zaman lafiya a Damaturu da jihar baki daya.