Shugaban jam’iyyar APC ya koma ofishinsa

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, ya koma bakin aikinsa tare da shiga ofishinsa a matsayin shugaban jam’iyyar. An dai kulle ofishin ne na wasu makonni bayan umarnin kotu na dakatar da shi daga shugabancin jam’iyyar, bayan ya halarci babbar sakatariyar jam’iyyar an bude masa ofishinsa don gudanar da aiyukansa. Shugaban jam’iyyar, Adams Oshimohle, […]

Shugaban jam’iyyar APC ya koma ofishinsa

Adams Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, ya koma bakin aikinsa tare da shiga ofishinsa a matsayin shugaban jam’iyyar.

An dai kulle ofishin ne na wasu makonni bayan umarnin kotu na dakatar da shi daga shugabancin jam’iyyar, bayan ya halarci babbar sakatariyar jam’iyyar an bude masa ofishinsa don gudanar da aiyukansa.

Shugaban jam’iyyar, Adams Oshimohle, ya halarci wurin taron koli na jam’iyyar ranar Talata, ya ce an dage haramcin da aka yi wa mataimakin shugaban jam’iyar a yankin Arewa maso Yamma Senata Lawal Shu’aibu da kuma mataimakinsa Abdulkadir Inuwa domin samun zaman lafiya a jam’iyyar.