Shugaban JIBWIS na Kano ya fara biyan kudin masallaci
A ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kungiyar Izala a Jihar Kano (JIBWIS), Shaikh Dokta Abdullahi Saleh Fakistan ya mayar da Naira dubu 500, kudin ginin Masallacin Shaikh Ja’afar Mahmood Adam da ke Unguwar Sabuwar Gandu wanda ya karba bashi daga asusun ginin masallacin a can baya. Biyan kudin ya biyo bayan umarnin Ja’afar […]
A ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kungiyar Izala a Jihar Kano (JIBWIS), Shaikh Dokta Abdullahi Saleh Fakistan ya mayar da Naira dubu 500, kudin ginin Masallacin Shaikh Ja’afar Mahmood Adam da ke Unguwar Sabuwar Gandu wanda ya karba bashi daga asusun ginin masallacin a can baya.
Biyan kudin ya biyo bayan umarnin Ja’afar da Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Lemo ta ba Shugaban Kungiyar ta Izala tun a watan Yulin da ya gabata.
Duk da cewa Shehin malamin bai iya biyan dukkanin kudin da ake bin nasa ba, amma ya biya wani yanki na kudin tare da alkawarin biyan sauran Naira dubu dari hudu a wani lokaci nan gaba.
Tunda farko wani mutum ne mai suna Ahmad Muhammad ya shigar da kara inda ya nemi kotun ta tilastawa Shugaban JIBWIS din na Kano ya biya kudi Naira dubu 900, wanda ya karba daga hannunsa wanda kuma mallakar asusun ginin masallacin ne.
Mai karar ya shaida wa kotu cewa Dokta Abdullahi Fakistan ya karbi bashin Naira miliyan daya da dubu dari uku daga asusun ginin masallacin sai dai ya biya Naira dubu dari hudu daga ciki yayin da ya gaza biyan sauran kudin.
A cewar mai karar, ya yi iya kokarinsa akan Shugaban na Izala ya biya kudin amma abin ya gagara, wadda hakan ya sa ya yi karar sa gaban kotu don ta tilasta masa ya mayar da kudin.
A lokacin da yake bayar da kudin ta hannun lauyoyinsa, Alkalin kotun Mai Shari’a Isma’ila Dalhatu ya umarci wanda ake kara da ya maido da kudin zuwa yau Juma’a, idan kuma hakan ba ta faru ba, kotun za ta iya daukar hukunci mara dadi a kansa.