Shugaban Kamaru ya yi bikin cika shekara 33 a kan mulki
Magoya bayan jam’iyyar RDPC ta Shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru sun yi bukukuwar cika shekara 33 da karbar mulkin kasar daga marigayi Ahmadou Ahidjo.A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka gudanar da bikin a duk fadin kasar. Sai dai bikin ya zo ne a wani lokacin da kasar take fuskantar barazanar tsaro daga […]
Magoya bayan jam’iyyar RDPC ta Shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru sun yi bukukuwar cika shekara 33 da karbar mulkin kasar daga marigayi Ahmadou Ahidjo.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka gudanar da bikin a duk fadin kasar. Sai dai bikin ya zo ne a wani lokacin da kasar take fuskantar barazanar tsaro daga kungiyoyin ’yan ta’adda wadanda suka zafafa hare-hare a lardin Arewa-mai-Nisa. Kodayake, kalaman da suke fitowa daga bakunan ’ya’yan jam’iyyar RDPC shi ne cewa a duk wannan tsawon shekarun da ya diba yana tafiyar da mulki, “Shugaba Paul Biya ya samu cimma wasu muradu da suka bai wa kasa samun daman ci gaba”. Daga cikin irin ababan da ya aiwatar, akwai samar da zaman lafiya, da shimfida akidar dimukaradiyya, da wasu manyan aikace-aikace da suka danganci karfafa samar da makamashin wutar lantarki a karkashin gina wasu madatsun ruwa, da kuma sabbin tashoshin jiragen ruwa a biranen Kribi a kudancin kasar da kuma Limbe a Kudu-maso-Yammacinta.
Har ila yau, abin da yake daure wa tarin jama’a shi ne dade wa kan mulki da wasu shugabannin kasashen Afirka suke yi.
Misali Shugaba Biya mai shekara 82 a duniya ya debi shekara 33 a kan kujerar mulki har a yanzu kuma tsarin mulkin kasar ya ba shi damar da ya sake neman shugabancin kasar. Hakazalika, akwai Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbazogo na kasar Ekuatorial Guinea mai shekara 73 a duniya, wanda ya kwashe shekara 36 a kan mulki. Wannan dadewar ta yi daidai da na Shugaba Eduardo Dos Santos na kasar Angola wanda yake da shekara 72 a duniya.
Sai dai shi kansa Shugaba Biya a wata amsar tambayar ga wani dan jarida, inda ya ce me ye dalilin da ya sa ya debi tsawon lokaci yana mulkar Kamaru, Mista Biya cewa ya yi : “Ba kowa ba ne yake samun damar dadewa a kan kujerar mulki face wanda ya isa.” Ya kara da cewa bai karbi mulkin kasar ba ta hanyar yin amfani da karfin tuwo, ko ta hanyar danniya.
Bugu da kari, shugaban ya bayyana cewa akwai wani zaben shugaban kasa a shekarar 2018. A lokacinne kuma duniya za ta sanya ido ko zai kara tsayawa takara, ko kuma zai yar da kwallon mangoro.