Jami’in Binance ya tsere daga hannun mahukuntan Nijeriya
Ofishin mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan tsaro ya ce yana aiki da kasashen waje domin sake cafke Mista Anjarwalla.
Ofishin Babban Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, ya tabbatar da tserewar wani jami’in kamfanin hada-hadar kudi na Binance, Nadeem Anjarwalla daga hannun jami’an tsaro.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin Babban Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Zakari U. Mijinyawa ya fitar a ranar Litinin.
- Harkar Noma Ce Kaɗai Za Ta Samar Da Zaman Lafiya A Najeriya — Peter Obi
- Gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin shari’a kan Binance
Ofishin ya ce tuni jami’an tsaron Najeriya suka fara aiki da ‘yan sandan kasa da kasa domin samun takardar sammacin da za a kama Anjarwalla.
Wanda ake zargin ya tsere ne bayan kotu ta bayar da umarnin tsare shi tsawon mako biyu, inda aka sanya ranar 4 ga watan Afrilu 2024, domin ci gaba da shari’arsa a gaban kotu.
A sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta bukaci duk wani mai karin bayani dangane da wanda ake zargin ya taimaka wa jami’an tsaro.
A gefe guda kuma, Gwamnatin Tarayya ta shigar da kara kan kamfanin Binance a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Hukumar Tara Haraji ta Kasa, FIRS ce ta sanar da matakin a cikin ƙar6ar da shigar mai lamba FHC/ABJ/CR/115/2024.
Gwamnatin dai na tuhumar kamfanin Binance da aikata laifuka huɗu da ke da alaka da kin biyan haraji.